Wasu masu ruwa da tsaki na jam’iyyar LP a Jihar Kaduna na bukatar shugabannin jam’iyyr na kasa da na jihar su gudanar da binciken asusun yakin neman jam’iyyar a zaben 2023, domin gano nawa aka kashe.
Wannan lamari ya tasho ne a wurin ganawar masu ruwa da tsaki na jam’iyyar wanda ya gudana a Jihar Kaduna.
A cikin wadanda suka halarci ganawar sun hada da mukaddashin shugaban jam’iyyar na jiha, Alhaji Isa Ciroma, mukaddashin sakataren jam’iyyar, Sani Musa Sahabi da kuma ‘ya takarar majalisar dattawa na Kaduna na kudu da na arewa, Mike Auta, Alhaji Sidi Bamali da dai sauran ‘ya’yan jam’iyyar.
- Bauchi Za Ta Gudanar Da Zaɓen Shugabannin Ƙananan Hukumomi A Watan Agusta
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Daliban Tsangaya 15 A Sakkwato
Da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan ganawar, Bamali wanda ke tare da sauran masu ruwa da tsaki, ya yaba wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Peter Obi bisa yadda ya bayar da bayanin asusun yakin neman zaben da ya zo ta hannunsa, ya kuma bukaci sauran shugabannin jam’iyyar a matakin jiha da na kasa da su yi koyi da shi.
Ya ce da alama an samu rashin shugabanci a jam’iyyar reshen jihar duk da cewa an yi sa’ar samun mataimakin dan takarar shugaban kasa, Datti Baba Ahmed da sakataren kungiyar da sauran manyan masu fada aji a matakin kasa da jiha.