Wani abu mai kama da sakaci da ya ɗaure kan al’umma da dama a Jihar Katsina shi ne, yadda ‘yan ta’adda suka yi wa wasu garuruwa ƙawanya suka yi masu kisan kare dangi a karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina.
Sai dai bayanan da suka biyo bayan wannan mummunan harin wuce gona da iri shi ne, irin yadda gwamnatin Jihar Katsina karkashin jagorancin Malam Dikko Umar Radda ta yi gum da bakinta a daidai lokacin da radadin kisan ke tafarfasa.
- Tinubu Ya Ba Jama’an Tsaro Umarnin Kamo Ƴan Ta’addan Da Suka Kashe Mutane A Katsina
- Za A Yi Sallah Babu Lantarki A Jahohin Kano, Jigawa, Katsina, Ma’aikatan KEDCO Sun Shiga Yajin Aiki
Ba tare da aune ba, sai dai ji aka yi tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takara shugaban kasa a zaben da ya gabata a karkashin jam’iyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yana jajanta wa al’ummomin da abin ya shafa, ita kuwa gwamantin Ji-har Katsina ta yi shiru.
Bullar wancan sanarwar tasa jikin jama’a da dama ya yi la’asar ganin cewa wani mutum daga nisan duniya ya fara nuna alhini kan wannan lamari, amma gwa-mantin Jihar Katsina tana nan gefe guda.
Alhaji Atiku ya ce ya yi mamakin yadda ‘yan bindiga ke da karfin halin kai wa ja-mi’an tsaro harin kwantan bauna har su kashe wasu daga ciki.
Yana mai Allah wadai da kuma tir da irin wannan lamarin da ke taruwa a Jihar Katsina da wasu jihohin arewacin Nijeriya tsawon lokaci abin ya ki karewa.
Kamar yadda rahotanni suka bayyana cewa an kashe fiye da mutane 50 a hare-haren wuce gona da iri da ‘yan bindiga suka kai ciki har da jami’an ‘yansanda hudu da kuma dakarun zaman lafiya na C-Watch guda biyu.
Rundunar ‘yansandan Jihar Katsina a ta bakin mai magana da yawunta, ASP Abu-bakar Aliyu ya yi taron manema labarai, inda ya bayyana yadda abin ya faru a bangaren jami’an tsaro. Ya ce an kashe jami’an ‘yansanda 4 da jami’an C-Watch 2 da Kuma mutane 20.
Ya kara da cewa lallai wannan harin abin takaici ne da bakin ciki, musamman irin yadda harin ya fi rutsawa da mata da kananan yara.
Kazalika, rundunar ‘yansanda ta ce tuni jami’an tsaro sun yi kawaye wajen da wannan lamari ya faru domin tabbatar da an kama wadannan suka yi wannan danyen aiki domin su girbi abin da suka shuka.
Sai dai kuma a cikin wani irin yanayi da sanyin jiki gwamantin Jihar Katsina ta fitar da sanarwa tana jajanta wa al’ummomin da wannan harin ya shafa a kauyen gidan Boka a karamar hukumar Kankara, inda ta ce an kashe mutane 26.
Sanarwar wanda mai taimaka wa gwamnan Jihar Katsina kan harkokin yada laba-rai, Ibrahim Kaula ya fitar, inda ya nuna takaici da wannan harin wuce gona da iri.
Sai dai sanarwar ta zo ne bayan da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya fitar da tashi wanda ake ganin kamar gwamantin Jihar Katsina ta yi fargar jaji.
Ibrahim ya ce gwamnatin Dikko Radda a shirye take wajen ganin ta kawo karshen wannan matsalar tsaro da ta-ki-ci-ta-ki cinyewa kuma ta kara nuna bukatar da ake da ita na ganin jama’a da su ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro da bayanai sirri domin ganin an samu nasara
Gwamna Radda dai ya sha nanata cewa ba zai taba yin sulhu da ‘yan bindiga ba, sai dai idan ‘yan bindiga sun ajiye makamansu, sun rungumi zaman lafiya.
Yanzu dai Jihar Katsina ta kara komawa wani sansanin daukar rai, inda kullum sai an kashe jama’a ko an sace, ko an kone gari da sauran nau’in zalunci ba dare ba rana.
A wani hari na ramuwar gayya kuma, rundunar sojin saman Nijeriya ta kashe ‘yan bnidiga 29 tare da ceto wadanda suka yi garkuwa da su ciki har da diyar sarkin ga-rin Ruwan Godiya.
An samu nasarar ne a wani hari ta sama da aka kai a kusa da tsaunin Bakori da Yartsintsiya a karamar hukumar Kankara ta Jihar Katsina.
Wannan farmakin ya gudana ne a matsayin na mayar da martani ga harin baya-bayan nan da aka kai a karamar hukumar Kankara a ranar Lahadi, 9 ga watan Yunin 2024, ya kuma dakile ayyukan ta’addanci a yankin.
Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa za ta ci gaba da hada kai da so-jojin kasa da hukumomin leken asiri don ganowa tare da kawar da masu aika ta laifuka a yankin.