Kungiyar dillalan masu sana’ar Bola-jari ta Nijeriya ta kasa, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta ba su lamuni mai sauki domin fadada harkokin kasuwancinsu.
Dillalan na jari-bola sun kuma bukaci gwamnati da ta yi duba kan hukumomin tsaro da su daina muzgunawa mambobinsu.
Shugaban shugabannin kungiyar, Alhaji Aminu Hassan, ne ya yi wannan roko a taron masu ruwa da tsaki na kungiyar a ranar Lahadi a Abuja.
Kungiyar ta masu sana’ar Bola-jari, kungiya ce da take da rijista a hukumance a karkashin dokar kungiyar kwadago, Cap. T14, na dokokin Tarayyar Nijeriya 2004.
Ita ce jigo ta duk mutanen da ke sana’ar Bola-jari, kuma take rarrabawa kamfanoni masu sarrafa lallatattun kaya su juya su zuwa sababbi kaya.
Masana sun ce sana’ar tana samun sama da Naira tiriliyan daya a duk shekara.
A cewar Hassan, kungiyar na matukar bukatar kudade da kariya domin bunkasa gudummawar da take bayarwa ga tattalin arzikin kasa.
“Muna da mambobi har miliyan biyar, amma suna aiki a cikin yanayi mai wahala,” in ji shi.
Hassan ya yi zargin cewa jami’an tsaro na cin zarafinsu “musamman wajen isar da kayayyakinmu ga kamfanonin da ke hakar man fetur”.
“Saboda haka, muna kira ga gwamnatin tarayya da ta shiga tsakani ta kuma taimaka mana wajen bin diddigin wannan mugunyar dabi’ar domin ba mu damar gudanar da harkokinmu ba tare da wata matsala ba.
“A jihar Kano kadai muna da mambobi kusan miliyan guda da suke bazuwa a fadin jihar ba a maganar jihar Legas inda muke da mambobi kusan miliyan biyu a sana’ar Bola-jari.
Shugaban ya kara da cewa “Kasuwancin da ke da dimbin mambobi sun cancanci tallafin kudi da kariya daga gwamnatin tarayya don ba su damar yin aiki yadda ya kamata.”
Hassan ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta sa baki kan farashin kayayyakin da suke sayar da su, kar a bar wa kamfanonin da suke kasuwanci da su.
“Wadannan kamfanoni, galibin kamfanonin kasashen waje, mallakar Sinawa da Indiyawa, suna sha’awar canza farashin kayayyakin da suke saya daga gare mu yadda suke so, wani lokacin ba tare da sanar da mu, masu kawo kayayyaki ba.
“Wannan ci gaban ya shafi kasuwancinmu sosai.
“Misali, za ku iya siyan kaya a kan Naira 500,000, amma idan kun isa kamfanin, za su ce muku ba za su iya siyan sa fiye da N400,000 ba.
“Wannan yakan haifar da babban rashi ko asara daga bangarenmu. Ka yi tunani bayan ka sayi samfur akan N500,000 kawai ka gama sai ka siyar da shi akan N400,000.