Masu sayar da kayan lemun roba da makamantansu sun koka kan rashin cikin da ake fama da shi wanda ke da alaƙa da yadda farashin kaya ke ci gaba da tashin gauron zabi.
Wani rahoto da kamfanin dillancin labaran Nijeriya na (NAN) ya fitar ga masu shaguna a Jihar Legas, ya bayyana cewa sun samu koma baya wajen samun cinikin da suka saba, saboda yadda kamfanoni suka kara kudi kayan su da ruwan roba da kaso 100.
- Yadda Shan Taba Ke Yi Wa Mata Mummunar Illa
- An Bukaci Tinubu Ya Nemi Kasashen Turai Su Yafe Wa Nijeriya Basukanta
Wasu Æ´an kasuwar sun ce an samu raguwar ciniki daga kashi 30 zuwa 50 a cikin 100 a halin yanzu.
NAN ta ruwaito cewar a shekarar da ta gabata ta 2023 ana sayar da kayan sha na roba mai girman 50cl a kan farashi N150 kowanne, amma kuma a yanzu ake sayar da roba É—aya ta lemu a kan Naira 300.
Kazalika a yanzu ana sayar da Malt kan N400 saɓanin N250 da ake saidawa a baya.
Wata mai suna Ngozi Ogbjnachara da ke da shago, ta ce a halin yanzu kasuwancin nasu babu wata riba sosai saboda hauhawar farshi da ake ta ƙara samu kan kayayyakin.
Ngozi da sauran takwarorinta Æ´an kasuwa sun yi kira ga masu ruwa da tsaki da kuma gwamnati kan É—aukar mataki game da tsadar kaya da ke ci gaba da tashin gauron zabi.
Wani rahoton ya nuna yadda aka samu ƙarin farshin kayan masarufi a watan Janairun 2024 da kaso 0.98 wato daga 28.92 a watan Disamban 2023 zuwa 29.90 a watan Janairun shekarar nan da muke ciki.