Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed ya yi zargin cewa ana yunkurin yi masa magudi a zaben gwamnan da za a gudanar a 2023.
Ya bayyana haka ne ranar Lahadi a gidan gwamnatin Jihar Bauchi yayin da kungiyar Kiristoci ta jihar ta kai masa ziyarar bikin Kirsimeti.
- Liverpool Ta Sayi Cody Gakpo Daga PSV
- Yahaya Bello Ya Ba Ma’aikata Hutu Saboda Buhari Zai Kai Ziyar Bude Wasu Ayyuka A Jihar Kogi
Leadership Hausa ta ambato Gwamna Bala Mohammed yana cewa mutanen da suke yunkurin yin amfani da karfin gwamnatin tarayya domin yin magudin zabe ba za su yi nasara ba.
Ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bari hakarsu ta cimma ruwa ba.
Bala Mohammed zai kara da dan takarar jam’iyyar APC, Siddique wanda tsohon babban sojan saman Nijeriya ne.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp