A Karshen tattaunawar da wakiliyarmu RABI’AT SIDI BALA ta yi da shahararren marubucin fim kuma mai shiryawa a cikin masana’antar Kannywood, wanda ya shafe shekaru goma yana rubuta fim wato Abba Harara, ya bayyana wa masu karatu ra’ayinsa dangane da fitowa matsayin jarumi, ya kuma yi karin haske game da yadda ya dauki fim a wajensa, tare da irin kalubale da nasarorin da ya samu, har ma da wasu batutuwan da suka shafi sana’arsa ta fim. Sannan ya ja hankalin masu sha’awar shiga harkar fim da su yi biyayya ga na gaba domin samun nasara. Ga dai tattaunawar kamar haka:
Kamar da wanne lokaci ka fi jin dadin yin rubutu?
Na fi jin dadin yin rubutu kamar da Asuba da kuma tsakiyar dare.
Wanne fim ne ya zama bakandamiyarka wanda ka rubuta da wanda ka shirya?
RUHIN MIJINA ne Bakandamiyata a fina-finai da na rubuta. A wanda na shirya kuma ‘MALAMIN KAUNA’ ne Bakandamiyata.
Ko akwai wani kalubale da ka taba fuskanta game da harkar rubutu ko kuma shirya fim?
Akwai kalubale da na fuskanta tabbas a game da rubutu da kuma shirya fim.
Kamar wadanne irin kalubale kenan?
Kalubalen da na fuskanta a rubutu shi ne a lokacin da na soma in na kai wa Furodusoshi’ ba sa karba haka ba sa kallon abin da kima kasancewar ba a sanni ba, sai da na sa juriya na yi hakuri sai gashi kuma komai ya zama labari. Haka kuma kalubalen da na fuskanta a shirya fim dina na farko ‘MALAMIN KAUNA’ gaskiya ba zai misaltu ba don ba zai fadu ba.
To batun nasarori fa?
Na samu nasarori hakika masu tarin yawa suma dai sirri ne.
Ko akwai wani fim da ka rubuta ko ka shirya wanda daga baya kake da ka sanin rubuta shi ko shirya shi sabida wasu dalilai?
MALAMIN KAUNA’ sunan fim din, ni na shirya shi Adamu Abdullahi ya rubuta, dalilin da ya sa na ji dama ban yi shi ba shi ne; na soma shi da kkarsashi amma a karshe na ji kawai na hakura da shi saboda wasu matsaloli da aka samu a dalilinsa.
A cikin fina-finan da ka rubuta ko ka shirya wanne ne ya fi shahara aka fi saninsa ya fi kuma daukar hankalin Jama’a?
Fim din shi ne ‘SIRRIN ZUCIYA’
Wadanne Jarumai ne suka fito a cikin fim din?
Ali Nuhu, Sultan Abdulrazak, Misbahu Anfara Daddy Hikima, ZPretty, Asmau Sani da dai sauransu.
Me kake son cimma game da sana’arka ta fim?
Ina so na kai matakin da duniya za ta amsa sunana haka duk abin da na yi ko na rubuta zai isar da sako a ko ina a fadin duniya, wannan shi ne burina.
Mene ne ra’ayinka game da fito wa matsayin Jarumi ko kuwa ka fi so ka tsaya a iya me rubutawa da kuma shiryawa?
Eh! Gaskiya ina da burin fara fito wa a matsayin Jarumi kuma nan ba da dadewa ba in sha Allahu zan fara fito wa a matsayin Jarumi.
Wanne abu ne ya taba faruwa da kai na farin ciki ko akasin haka wanda ba za ka taba iya mantawa da shi a rayuwarka ba?
Toh! Gaskiya abubuwan suna da yawa sai dai daya daga ciki shi ne; A kowacce rana mutane daban-daban wanda ban sani ba suna kira na su yi min fatan alkhairi da addu’a akan fim dina ‘MALAMIN KAUNA’, wannan shi ne babban abin farin cikin da na kasa mantawa da shi.
Shin Malam Abba ya na da aure ko kuwa tukunna dai?
A’a ba ni da aure tukunna dai (Dariya).
Ko akwai wadda ta taba kwanta maka a rai cikin masana’antar da har ta kai da kun fara soyayya tare?
Gaskiya babu wacce hakan ya taba faruwa tsakanin mu.
Misali wata a cikin masana’antar ta ce tana sonka za ta aure ka, shin za ka amince ka aure ta ko kuwa ba ka da ra’ayin hakan?
Eh! Zan yarda da hakan in dai ra’ayin mu ya zo daya da juna.
Wacce irin mace kake son aura?
Dariya! Na bar wa Allah zabi.
Yaushe za ka yi aure?
Aure lokaci ne duk san da ya zo mun zan yi shi, ni kaina ba na ce ga ranar ba.
Sai dai ba ka fada wa masu karatu shekarunka ba, za ka yi kamar shekara nawa yanzu?
Shekarata ashirin da takwas.
Ya ka dauki rubutun fim da kuma shirya fim a wajenka?
Su ne Ni, haka na dauki rubutu da shirya fim ba ni da kamar su, na dauke su matsayin sana’a.
Bayan wannan sana’ar da kake yi ta shirya fim da rubutawa, shin kana wata sana’ar ne?
Ba ni da wata sana’ a bayan fim.
Shin kana da Ubangida ko iyayen gida cikin masana’antar Kannywood?
Tabbas! ina da shi, Ali Rabiu Ali Daddy.
Waye Babban abokinka a cikin masana’antar Kannywood?
Babban Abokina shi ne; Salisu Yaro.
Wanne kira za ka yi ga masu kokarin shiga cikin harkar, har ma da wadanda suke ciki?
Su yi biyayya ga manyansu, sannan su yi hakuri da na gaba da su, kuma su yi abin da ya kawo su matukar suna so su yi nasara akan abin da suka sa gaba, wannan shi ne kirana ga ‘yan baya. Wadanda suke ciki kuma mu ci gaba da kyautata mu’amula kuma duk abin da zamu yi mu yi don Allah ba dan riya ba.
Wanne irin abinci da abin sha ka fi so?
Na fi son Sakwara miyar Agushi. Abin sha kuma Kunun Aya.
Wanne irin kaya ka fi son sakawa?
Na fi son Jallabiya.
Ko akwai wani kira da za ka yi wa gwamnati musamman na ganin ci gaban masana’antarku ta Kannywood?
Da a ce gwamnati za ta shiga cikin sha’anin Kannywood kuma ta saka hannun jari to da abin ya kara bunkasa ya kai duk inda ba a tunani amma wai a haka Gwamnati sai dai ta samu a jikin Kannywood wannan ba karamin abin kunya bane wallahi.
Me za ka ce ga makaranta wannan shafi na Rumbun Nishadi?
Ina godiya da jinjina a gare su Allah ya bar zumunci, su ci gaba da kasancewa da wannan shafi domin karanta gaskiya fiye da jita-jitar da za su ji a gari, domin kuwa wannan shafi kai tsaye yake kawo muku gaskiyar lamarin daya shafi duk wani dan fim ko mawaki ku ci gaba da kasancewa da wannan shafi na Rumbun Nishadi domin nishadantarwa.
Me za ka ce da ita kanta Jaridar Leadership Hausa?
Ina rokon Allah ya kara daukakata ta ci gaba da haskawa a ko ina a fadin duniyar nan.
Ko kana da wadanda za ka gaisar?
Eh! Ina gaida Ali Rabi u Ali, Salisu S. Fulani, Nasir Nid, Muhammad Dan Buzu, Ibrahim Bala, Abdul Sahir, Nasir Naba, Zahra Daimond, Humairatuh, Khadija Yobe da sauransu.
Muna godiya Malam Abba
Ni ma na gode Malama Rabi’at.