Masu yi wa kasa hidima su takwas da masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Zamfara, sun shafe kwanuka 32 a hannun masu garkuwar.
An yi garkuwa da su ne a yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa sansanin su na yi wa kasa hidima da ke a jihar Sokoto.
- Tabbatar Da Tsaro A Jihar Zamfara
- Dusa Muke Ci Muke Rayuwa Saboda Tsananin Rashin Tsaro – Mazauna Wani Yankin Zamfara
LEADERSHIP ta rawaito cewa, an sace su ranar 17 ga watan Agusta bayan sun dawo daga jihar Oyo zuwa jihar Sokoto.
Masu garkuwar sun bukaci karin Naira miliyan 200 a matsayin kudin fansa baya ga Naira miliyan 13 da suka karba daga wurin iyayen masu yi wa kasa hidima a matsayin kudin fansa.
Idan ba a manta ba, tun da farko iyayen na su sun baiwa masu garkuwar Naira miliyan 5, inda aka ci gaba da tattaunawa kan kudin fansar ta su Naira miliyan 13 wanda masu garkuwar suka baiwa iyayen wa’adin ranar 6 ga watan Satumba na su biya sauran kudin fansar Naira miliyan 8.
Mai magana da yuwun NYSC, Eddy Megwa, ya ce, mahukuntan NYSC na kan kokari don ganin an ceto masu yi wa kasa hidima daga hannun barayin mutanen.