Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Guo Jiakun, ya ce zuba jari a Sin, da cimma nasarar more riba a nan gaba, batu ne da daukacin masu zuba jari na kasa da kasa suka amince da yiwuwarsa.
Guo, wanda ya bayyana hakan a Larabar nan, ya ce Sin na maraba da masu kamfanoni daga dukkanin sassan duniya, da su shiga a dama da su a tsarin zamanantarwa irin na Sin, da cimma manyan nasarori tare, da ingiza ci gaba ta hanyar dunkule matakan samar da ci gaba mai inganci.
Jami’in ya ce, ya zuwa watan Maris na bana, masu zuba jari sun yi rajistar jimillar kamfanoni miliyan 1.24 a kasar Sin, inda suka zuba jarin da ya kusa dalar Amurka tiriliyan 3. A gabar da suke mara baya ga sauye-sauye da bude kofa da Sin ke aiwatarwa, masu zuba jarin sun samu karin damammakin gina kai da tarin riba mai yawa.
A yayin taro karo na uku, na baje kolin tsarin rarraba hajojin masana’antu na duniya da aka kammala ba da jimawa ba, adadin sassa da suka baje hajoji ya karu daga kasashe 55 da yankuna daban daban, zuwa 75 a zangon farko na gudanarsa.
Cikin adadin, yawan masu nuna hajoji daga Amurka ya karu da kaso 15 bisa dari, idan an kwatanta da wanda ya gabata, ya kuma kasance kan gaba a yawan masu baje hajoji daga ketare. A fannin yawan manyan kamfanoni kuwa, sama da kaso 65 bisa dari na masu baje hajojin, na cikin manyan kamfanoni da jagororin masana’antu 500 mafiya girma a duniya. Matakan da suke dauka na zahiri, sun nuna amincewar da kamfanoni masu jarin waje suka yi da makomar tattalin arzikin kasar Sin. (Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp