ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Monday, December 22, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mata A Dage Da Tsare Mutuncin Kai – Zainab Muhammad

by Bilkisu Tijjani
2 years ago
Mata

LABARAI MASU NASABA

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

ADVERTISEMENT

ZAINAB MUHAMAD mai neman ilimi kuma ‘yar kasuwancin sayar da kayan kamshi na mata ‘yar asalin Garin Hadejia ta yi wa shafi Adon Gari karin haske kan yadda ta tsinci kanta a harkar kasuwaci wanda ta ce ta samu rufin asiri sosai a cikinta, sannan ta yi kira ga mata da su koyi sana’a domin su tsira da mutuncinsu, kamar yadda za ku ji a wannan hira da wakiliyarmu BILIKSU TIJJANI KASSIM.

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki

Suna na Zainab Muhammad Sambo, ni cikakkiyar ‘ya Hadejia ce an haife ni a Garin Hadejia a shekara ta 1997 a Unguwar Wuriwa, na yi makaranta a Garin Hadejia

Shin Zainab matar aure ce?

A’a ni ba matar aure bace muna niyya in sha Allahu.

‘Yar kasuwa ce ko ma’aikaciya?

A a ni ba ma’aikaciya bace, ina dan taba kasuwanci haka-kadan dai wanda ba’a rasa ba.

Wanne irin kasuwanci kike yi?

Kayan kamshi nake sayarwa

Shin me kasuwancin naki ya kunsa?

Kamar turaren wuta, Humura da duk nau’ika na kayan kamshi da sauransu.

To ke kuwa me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwanci?

Saboda ni ma’abociyar san kamshi ce.

Me ye matakin karatunki?

Na gama Difiloma.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?

Kalubalan da na fuskanta akwai ranar da wata ta sani na hada mata turaren wuta amma ba ta saya ba shi ne kalubale na da na taba fuskanta, saboda abin ya bani haushi kin san dai yadda hadin turare yake da wahala ka kwana kana yi sai da na gama ba ta kara magana ba.

Zuwa yanzu wanne irin nasarori kika cimma?

Na samu nasarori da dama bikin kawayena da taron makaranta duk da sana’ ata nake yi har na tallafa wa mabukata

Wanne abu ne ya fi faranta miki rai game da sana’arki?

Alhamdu lillah idan na yi turare a ce ya yi dadi ana so wannan yana faranta min rai ina jin dadin haka sosai.

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?

Ta hanyar intanet kamar whatsapp, facebook, instagram, da dai sauransu.

Dame kike so mutane su rika tunawa dake?

Ina so mutane su rika tunawa da ni a kan kamshina da kuma fara’a ta da wasa da dariya.

Ga karatu, ga kuma kila kina taya mama ayyukan gida, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?

Kome nawa a tsare yake komai na ba shi lokacinsa.

Wace irin addu’a ce idan aka yi miki kike jin dadi?

In aka min addu’ar Allah ya jikan mahaifina ina jin dadi sosai

Wane irin goyon baya kike samu daga wajen iyaye da ‘yan uwanki?

 Alhamdu lillah ina samun goyan baya dari bisa dari a wurin iyayena da ‘yan uwana babu abin da zan ce musu sai godiya da kuma addu’ar Allah ya saka musu da alkhairi.

Kawaye fa?

Ni ban da kawaye, ‘yan uwana su ne kawayena

Me kika fi so cikin kayan sawa fa kayan kwalliya?

Ina son leshi da doguwar riga ta komai kayan kwalliya kuma ba na son na ga idona babu kwalli.

A karshe wace irin shawara za ki bawa ‘yan uwanki mata?

Shawarata ga mata ‘yan uwana su dage su nemi sana’a kuma su tsare mutumcinsu.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Maganin Sanyi Na Mata (Infection)?

October 19, 2025
Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?
Adon Gari

Ko Kin San… Yadda Za Ki Gyara Kanki Da Kanki?

October 12, 2025
tusar gaba
Adon Gari

Ko Kin San… Dalilin Da Ke Sa Mata Ke Ganin Farin Ruwa Kafin Ko Bayan Al’adarsu?

August 31, 2025
Next Post
Sanata Iya Abbas Ya Jajantawa Mutanen Da Iftila’in Iskar Hadarin Ruwa Ta Shafa A Hong

Sanata Iya Abbas Ya Jajantawa Mutanen Da Iftila'in Iskar Hadarin Ruwa Ta Shafa A Hong

LABARAI MASU NASABA

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja

Gwamnatin Tarayya Ta Tabbatar Da Ceton Dukkan Ɗalibai 230 Da Aka Sace A Neja

December 22, 2025
Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

Gobara Ta Haddasa Mummunar Asara A Kasuwar Kayan Katako A Kano

December 22, 2025
An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

An Sako Ragowar Ɗalibai Da Malamai Da Aka Sace A Makarantar Katolika Ta Neja

December 21, 2025
Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

Raphinha Da Yamal Sun Ci Ƙwallaye Yayin Da Barcelona Ta Doke Villarreal

December 21, 2025
Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

Davido Zai Raƙashe A Bikin Buɗe Gasar AFCON 2025 A Morocco

December 21, 2025
Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

Yankin Rijiyoyin Mai Na Teku Mafi Girma Na Kasar Sin Ya Ba Da Rahoton Yawan Mai Da Iskar Gas Da Ya Fitar A Shekara

December 21, 2025
An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

An Bukaci Bunkasa Fannin Kiwo A Hadin Gwiwar Sin Da Afirka

December 21, 2025
Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

Akpabio, Ganduje, Ogundoyin Sun Halarci Naɗa Seyi Tinubu Sarauta

December 21, 2025
Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

Tashar Teku Ta Ciniki Mai ‘Yanci Ta Hainan Ta Bude Sabon Babin Hadin Gwiwar Sin Da Kasashen Afirka

December 21, 2025
Tinubu

Dambarwar Naɗa Muƙamai Da Soke Su A Gwamnatin Tinubu

December 21, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.