Aisha Seyoji matashiyar ‘yar kasuwa kuma magidancinya mai kokarin neman na kanta ta shawarci mata da ke zaune a gidajen mazajensu da su kyautata hakuri a zamantakewar aure, tare da neman na kansu domin tsira da mutuncinsu. Ta ba da wannan shawara ce a tattaunawarsu da wakiliyar LEADERSHIP BILIKSU TIJJANI KASSIM. Baya ga haka ta bayyana irin nasarar da ta samu a kasuwancinta, ga dai yadda hirar tasu ta kasance:
Da farko masu karatu za su su ji sunanki da kuma dan takaitaccen tarihinki
Sunana Aisha Seyoji. An haife ni a Garin Gombe, na yi Firamare da jami’a duka a Bauchi.
Yaya batun aure da iyali a warinki?
Ina da aure da ‘ya’yana uku.
A halin yanzu masu karatu na bukatar su san shin kina aiki ne ko karatu ko kuma sana’a, wane mataki kike ko zaman gida kike?
Toh Alhamdulillah, Ina aiki, ina kasuwanci, a kasuwancin ina saida kusan duk wani nau’i na abin da ya shafi kayan kamshi.
Shin ko za mu iya sanin abin da ya jawo hankalinki kan wannan sana’a?
Abin da ya ja hankalina na fara wannan sana’a ta kayan kamshi, gaskiya na kasance ma’abociyar son turare kama daga na jiki, na kaya da na gida. Wannan soyayya da nake da ita ga kamshi ya sa na fara sha’awar sana’ar kayan kamshi, Allah cikin ikonsa na hadu da wata baiwar Allah a Kano wanda itama tana kasuwanci kuma kusan komai tana saidawa ciki har da turaruka, nan dai na nuna mata sha’awata na son sanin yadda abin yake, daga nan ta fara nuna min, sannu a hankali kuma yanzu cikin hukuncin Allah sai gashi ina da shago nawa na kaina wanda ake saida kayan kamshi.
Ta wacce hanya kikebi wajen tallata sana’aki?
Eh to ba wata hanya ba ne sai ta intanet, a gaskiya na fi saida kayana ta Whatsapp, Instagram, Facebook da dai sauransu, sai kuma mutanena haka na gida da waje.
Shin ko akwai wata hanya da kike ganin gwamnati za ta iya shigowa cikin wannan sana’a taki ta tallafa domin a samu karin masu yi don Samar da aikinyi?
Eh sosai ma kuwa, gwamnati za ta iya shiga ciki ta taimaka, misali a ce irin shirye-shiryen gwamnati da suke yi na ‘Empowerment’ wato tallafi da ake ba wa jama’a domin kama sana’a su dogara da kansu.
Ko za ki bayyana wa mai karatu wani abu da ya taba faruwa da ke a rayuwa na farin ciki ko akasinsa da ba za ki taba mantawa ba?
Alhamdulillah gaskiya abubuwa na farin ciki da yawa sun faru wanda ba abin da zance wa Allah sai dai godiya. Rasuwar mahaifiyata shi ne ba zan taba mantawa da shi ba.
Ko kina da shawara da za ki ba wa mutane game da sha’anin rayuwa ta yau da kullum wanda idan suka yi koyi ko amfani da ita, rayuwa za ta inganta?
Shawarata ga al’umma itace, a duk inda muka tsinci kanmu mu rika tuna Allah farko, mu rike gaskiya da amana, tausayi da jinkan na kasa damu.
Idan muka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a yanzu, me za ki ce wa iyaye a kan muhimmancin tarbiyya kasancewar su kansu wadannan ‘ya’ya amana ce Ubangiji ya ba mu kuma zai tambaye mu a kan yadda muka tafiyar da su?
Tabbas iyaye mu ji tsoron Allah, mu sani cewa ‘ya’ya wata amana ne da ubangiji ya bamu kuma tabbas zai tambaye mu ta yadda muka tarbiyantar da su, mu yi kokari mu cire son zuciya mu rika gaya wa ‘ya’yanmu gaskiya ta hanyar nasiha da tunatarwa, mu koya musu sanin muhimmanci gaskiya, hakuri, juriya tawakkali, da kuma dogaro da kai.
Wace shawara za ki ba wa matan aure akan rayuwar aure duba ga irin zamanin da muke ciki?
Gare mu ‘yan uwa mata. Hakuri, hakuri mu kara akan wanda muke yi, mu kasance masu juriya da wadatar zuciya sannan uwa uba abin da ya fi muhimmanci ita ce addu’a.
A karshe zan mika sakon godiya ta musamman ga wannan gidan jarida na LEADERSHIP da ya bani damar kasancewa tare da ita a wannan tattaunawa, jinjina ta musamman gareki Hajiya Bilkisu.