A ranar Asabar ɗin makon da ya gabatar ne, Sheik Shamsudeen Kasim Abujummala Shugaban Majalisar Malamai na ƙaramar hukumar Sabon gari na ƙungiyar Izala, ya gabatar da wata lakca Mai taken ” Tsoron Allah” a Makarantan Nurul Islam da ke Unguwar Makera Hayin Dogo Samaru Zariya.
A lokacin da yake jawabi a gun taron, Sheik Abujummala ya baiyyana cewar, ya kamta ace mata sunfi kowa jin Tsoron Allah, sakamakon sunfi maza zuwa Makaranta da wuraren aikata Alkairi, musamman a wannan zamanin.
Sai dai daga bisani ya nuna takaicinsa abisa yadda aka sami akasin hakan, a Mai makon suka kasance jagaba wajen lallacewar wannan Al’umma.
- Abinda Ya Kamata Kusani Akan Wasan Arsenal Da Manchester City
- Peng Liyuan Ta Halarci Bikin Mika Lambobin Yabo A Fannin Raya Ilimin Yara Mata Da Mata Na Hukumar UNESCO
Sheihin Malamin ya ce da za a sami akalla Kashin 75 cikin ɗari na Mata su Gyara alaƙarsu da Allah da kowa ya canza, domin mafi yawan manyan kaba’irori, da ake aikatawa Mata na taka muhimmiyar rawa a Cikin.
Don haka Sheik Abujummala ya jawo hankalin Mata da su kasance masu jin Tsoron Allah a duk inda suka kasanca, da kuma nuna tausayi ga ƙananan yara koda basu Suka haifesu ba, Hakanan ya umurcesu da nuna ƙauna ga junansu tare da aikata umurnin Allah (swt)
Haka nan a nasa ta’alikin da ya gabatar Malam Abubakar Abba Dewu ya jawo hankalin Malaman Islamiyoyi, domin su kasanca masu shirya irin wadanan muhadirorin lokacin Bayan lokacin a Makarantun su, domin cusawa Mata da ƙananan yara jin Tsoron Allah tare da yin abin da ya dace da koyarwar addinini Musulunci a bisa sunnar Annabi Muhammad (saww).
Haka nan a lokacin da take miƙa jawabi godiya a gun taron Shugaban Makaranta Malam Halima Musa ta ce, suna shirya irin wannan muhadaran ne lokaci bayan lokacin sabo da cusawa Mata da ƙananan yara tsoron Allah a zukata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp