Wata Babbar gada da ke kan Babbar hanyar Gombe zuwa Bauchi ta sake ruftawa biyo bayan mamakon ruwan sama da aka yi a safiyar Lahadi, lamarin da ya dakile matafiyan daga tafiyarsu.
Wakilinmu ya rahoto cewa, gadar da ke kan hanyar Gombe zuwa Bauchi a kauyen Bara tana yawan ruftawa kusan duk lokacin damina, lamarin da ke kawo cikas ga zirga-zirgar matafiya na jihohin biyu da ke makwabtaka da juna.
Matafiyan sun koka kan cewa, a shekarar da ta gabata, gadar ta bangare har gida Uku, amma gwamnatocin jihohin Bauchi da Gombe sun kasa gyara ta yadda zata yi aminci sabida ganin kyashin cewa, gadar tana kan hanyar gwamnatin tarayya ce.
Sai dai a kwanakin baya, gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya na shirin sake gina hanyar da ta lalace cikin watanni shida masu zuwa.
Ya ce, ya samu tabbaci daga gwamnatin tarayya kan aikin, inda ya tabbatar da cewa yana daga cikin ayyukan da gwamnatin shugaba Bola Tinubu za ta aiwatar a shiyyoyi shida na siyasar kasar nan.