A ranar Alhamis ne mataimakin firaministan kasar Sin He Lifeng ya gana da babban shugaban kamfanin Citigroup a birnin Beijing.
A ganawar tasu, He Lifeng ya bayyana cewa kasar Sin tana zurfafa gyare-gyare a tsarinta na harkokin kudi, kuma za ta ci gaba da fadada shirinta na manyan hanyoyin bude kofa guda biyu da take da su a sashenta na kudi.
- Nijeriya Na Iya Samun Naira Tiriliyan 6.9 Na Kudin Shiga Daga Mai A Wata Daya
- Masu Harkar PoS Sun Bayyana Dalilin Karin Kudin Cire Kudi
Ya kara da cewa, kasar Sin tana lale marhabin da kamfanoni da cibiyoyin hada-hadar kudi da masu jari na dogon zango na kasashen waje, ciki har da Citigroup domin su zuba jari da gudanar da kasuwancinsu a kasar Sin da kuma samar da damammaki da shiga a dama da su wajen ciyar da kasuwar hada-hadar kudin kasar gaba.
Da yake nasa jawabin, Fraser ya ce, Citigroup na da kyakkyawan fata game da makomar tattalin arzikin kasar Sin da kasuwar hada-hadar kudinta, kuma yana son kara yin nazari a kan kasuwannin kasar Sin, tare da ba da gudummawa wajen inganta hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya tsakanin Amurka da Sin, da tabbatar da kiyaye ci gaban tattalin arzikin duniya mai inganci. (Abdulrazaq Yahuza Jere)