Mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang ya bukaci kasashen duniya su daukaka tsarin cudanyar kasa da kasa ko bangarori daban daban, da inganta ci gaba ta kowacce fuska kuma bisa adalci.
Ding Xuexiang ya bayyana haka ne a jiya Talata, cikin jawabin da ya gabatar ga taro kan tattalin arzikin duniya na 2025 a Davos na Switzerland.
- Kwangilar Tashar Wutar Mambila: Obasanjo Zai Bayar Da Shaida A Kotun Paris Yau
- Saudiyya Ta Ware Dala Biliyan 100 Don Sabunta Masallatan Harami
Firaministan ya kuma ba da wasu muhimman shawarwari 4. Na farko, ya yi kira ga kasa da kasa da su ingiza dunkulewar tattalin arzikin duniya ta yadda kowa zai ci gajiya, kana su yi kokarin samar da mafita ta moriyar juna kuma wadda kowa zai amfana da ita, bisa hadin gwiwar moriyar juna ta hanyar tattaunawa.
Ya kuma yi kira ga kasa da kasa da su daukaka tare da aiwatar da cudanya ta hakika a tsakaninsu, da kuma daukaka tsarin huldar kasa da kasa na MDD.
Ding Xuexiang ya kara da cewa, ya kamata kasashen duniya su hada hannu wajen samar da sabbin abubuwa da karfin ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya, da kyautata hadin gwiwa a tsakaninsu kan kirkire-kirkiren kimiyya da fasaha.
Ya kuma yi kira ga kasa da kasa da su hada hannu wajen shawo kan kalubalen duniya, kamar na sauyin yanayi da wadatar abinci da makamashi. (Fa’iza Mustapha)