Bisa goron gayyatar da gwamnatocin kasashen Guinea da Saliyo suka ba shi, Liu Guozhong, mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin wanda kuma shi ne mataimakin firaministan gwamnatin kasar, zai kai ziyara kasashen Guinea da Saliyo daga yau Litinin 10 zuwa 16 ga watan da muke ciki.
Sannan, bisa gayyatar shugaban kasar Guinea Mamady Doumbouya, Mr. Liu Guozhong zai kuma halarci bikin kaddamar da mahakar karafa ta Simandou a kasar ta Guinea, a matsayin wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping. (Lubabatu Lei)














