Mataimakin firaministan kasar Sin Liu Guozhong, ya yi kira da a gaggauta samar da sabbin fasahohin kimiyya a fannonin aikin gona da kiwon lafiya, da karfafa cin gashin kan fasahar kirkire-kirkiren magunguna da na’urorin likitanci.
Liu, mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya bayyana hakan ne yayin ziyarar bincike da ya kai lardin Guangdong da ke kudancin kasar Sin daga ranar Alhamis zuwa Asabar da ta gabata.
Ya jaddada cewa, ya zama wajibi a mai da hankali kan bukatu na gaggawa da ake da su a bangaren masana’antar da kuma ba da karfi ga muhimman fannoni kamar masana’antar fasahar samar da iri, da injunan noma, da kayan abinci, da fasahar shuka da kiwo.
Liu ya kuma yi kiran gaggauta yin gyarar fuska ga nasarorin da aka samu a fannin fasahar aikin gona, da karfafa aikin gona ta amfani da basirar zamani a aikace, da kara zurfafa sarrafa kayayyakin amfanin gona, da karfafa jagorancin samar da ayyukan yi da horarwa a kan dabarun aiki, don taimaka wa mutanen da aka tsamar daga kangin talauci, da ma’aikatan yankunan karkara wajen ci gaba da samun aikin yi ba tare da tangarda ba. (Mai fassara: Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp