Jagoran kula da harkokin tattalin arziki da kasuwanci na kasashen Sin da Amurka a bangaren Sin, wanda kuma shi ne mataimakin firaministan kasar Sin, He Lifeng, ya zanta da sakataren baitulmalin Amurka, Scott Bessent, ta kafar bidiyo jiya Jumma’a 21 ga wata, inda suka yi musanyar ra’ayoyi kan wasu muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arzikin kasashen biyu, bisa matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma.
Bangarorin biyu duk sun amince da muhimmancin alakokin tattalin arziki da kasuwanci a tsakaninsu, inda suka yarda su ci gaba da tuntubar juna kan batutuwan da suka fi daukar hankulansu.
Har wa yau, kasar Sin ta nuna matukar damuwa kan matakin da Amurka ta dauka kwanan nan, na kara sanya wa hajojin kasar Sin harajin kwastam. (Murtala Zhang)