Mataimakin firayin minista kuma ministan kiwon lafiya na kasar Thailand Anutin Charnvirakul, ya ce bayan gwamnatin kasar Sin ta kyautata manufofin kula da harkokin shige da fice a kasar, kasar Thailand ta kasance mafi samun karbuwa a tsakanin Sinawa masu yawon shakatawa, lamarin da ya burge al’ummar kasarsa matuka.
Anutin Charnvirakul wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai na CMG, ya kara da cewa, Sinawa sun shafe lokaci mai tsawo suna son zuwa Thailand bude ido, kuma a yanzu sun samu damar sake ziyartar kasar, lamarin dake da babbar ma’ana ga Thailand din, saboda zai taimakawa kasar tabbatar da farfadowar tattalin arziki sakamakon tasirin yaduwar annobar COVID-19, tare kuma da nuna al’adu na musamman na Thailand ta hanyar raya sana’ar yawon shakatawa. (Mai fassarawa: Jamila)