Gwamnatin Jihar Bauchi ta karyata rahoton da aka yada a kafafen yada sadarwa kan cewar mataimakin gwamnan Jihar, Sanata Baba Tela ya yi murabus daga mukaminsa.
A wata sanarwar da sakataren watsa labarai na ofishin mataimakin gwamnan Sani Mu’azu Ilelah, ya fitar a ranar Alhamis, ya bayyana cewar labarin karya ce kawai da marubucin ya kirkira ya kuma yada bisa manufarsa.
- Addu’a Ce Mafita Kan Matsalar Tsaron Nijeriya – Etsu Nupe
- An Kara Nuna Shaidu Kan Makircin NATO Na Lalata Duniya
Ya ce, “Domin cire kokonto, muna tabbatar wa al’ummar jihar Bauchi da ma kasa baki daya cewa, mataimakin gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Baba Tela bai yi murabus a matsayin mataimakin gwamnan Jihar Bauchi ba”
Ya ce, har yanzu Baba Tela na biyayya dari bisa dari ga manufofi da tsare-tsaren gwamantin jihar Bauchi a karkashin jagorancin gwamna Bala Muhammad.
Daga bisani Ilelah, ya bukaci al’ummar jihar da su yi watsi da wannan rahoton tare da gargadin masu yadawa da su daina.
“Mataimakin gwamnan ya jaddada aniyarsa na ci gaba da mara baya ga gwamna. Muna gargadi ga masu kokarin janyo rashin jituwa a tsakani da su gaggauta dainawa.”