ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kara Nuna Shaidu Kan Makircin NATO Na Lalata Duniya

by CMG Hausa
4 years ago
NATO

Wani sabon daftarin dabarun da aka zartas, a taron kolin kungiyar tsaro ta NATO da aka shirya a ranar 29 ga wata a birnin Madrid, ya ambato kasar Sin a karon farko, inda aka yi wa kasar Sin kazafi a matsayin “kalubale kan yankin Turai da na Atlantika”.

Wannan wata babbar shaida ce da ke nuna cewa, NATO tana jujjuya baki da fari don kirkirar abokan gaba, hakan ya tabbatar da cewa, kungiyar NATO da ta ragu bayan yakin cacar baka, kalubale ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

  • Bai Dace Amurka Ta Ci Gaba Da Karya Dokokin Cudanyar Kasa Da Kasa Ba

“NATO kawai kariya ce ta Amurka.” Jaridar Le Soir ta kasar Belgium ta yi nuni da hakan. Idan aka waiwayi yunkurin kafuwar kungiyar NATO da kuma yadda aka fadada kungiyar, ba abu ne masu wahala a ga cewa, kungiyar wani makami ne da Amurka ke amfani da shi wajen kafa kungiyoyi da kuma yin arangama ba.

ADVERTISEMENT

Idan aka kara yin la’akari, kungiyar NATO ta sake taka rawa wajen damfarar siyasa, bayan da Amurka ta sanya kasar Sin a matsayin “babbar ‘yar takarar ta”. Kwanan baya, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya yi ikirarin a cikin jawabinsa kan manufofin kasar game da Sin cewa, “za a tsara” muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen kasar Sin.

Taronkolin NATO na bana, ya gayyaci shugabannin Japan, Koriya ta Kudu, Australia da New Zealand a karon farko, da nufin kafa wata kungiyar NATO mai “Sigar Asiya-Pacific”, da kuma “tsara” wani muhalli bisa manyan tsare-tsare a kewayen kasar Sin, wanda ya kasance wani yunkuri ne mai hadari, na gabatar da wani mummunan aiki na kirkirar abokan gaba a yankin Asiya-Pacific.

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Kasar Sin ba ta taba tsoma baki cikin harkokin cikin gidan wasu kasashe ba, kana ba ta fitar da akidu zuwa kasashen waje, kuma ba ta shiga cikin ikon mallaka na sauran kasashe, ko tilastawa saura a fannin tattalin arziki, ko saka takunkumi ta bangare daya, ta yaya za ta iya kawo “kalubale” ga NATO? Sabanin haka, kungiyar NATO ta yi ikirarin cewa, ita “kungiyar tsaro” ce, amma a zahiri ta karya alkawarinta na kara fadada zuwa gabas, tana kuma tsallake kwamitin sulhun MDD akai-akai, don kaddamar da yaki da kasashe masu mulkin kai, inda ta zama wata ainihin “kungiyar mahara”. (Mai fassara: Bilkisu Xin)

NATO
CMG Hausa
+ postsBio
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugabannin Kasashen Duniya Sun Yi Wa Sin Fatan Alheri A Sabuwar Shekara
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    San Francisco sabon mafarin hadin gwiwar Sin da Amurka ne
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Xi Ya Halarci Kwaya-Kwaryan Taron Shugabannin Mambobin APEC
  • CMG Hausa
    https://hausa.leadership.ng/author/cmg-hausa/
    Shugaban Kasar Sin Ya Gabatar Da Rubutaccen Jawabi Ga Taron Jagororin Masana’antu Da Kasuwanci Na APEC

MASU ALAKA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5
Daga Birnin Sin

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana
Daga Birnin Sin

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi
Daga Birnin Sin

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Next Post
Fintiri Ya Dauki Shugabar Jami’ar Jihar Adamawa, Mataimakiyarsa

Fintiri Ya Dauki Shugabar Jami'ar Jihar Adamawa, Mataimakiyarsa

LABARAI MASU NASABA

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026
Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Han Zheng Ya Halarci Baje Kolin CIFIT Karo Na 26 Tare Da Gabatar Da Jawabi

September 8, 2026
Wani Soja Ya Kashe Kansa Bayan Kashe Matarsa A Jihar Neja

Kano Za Ta Kafa Sansanonin Sojoji A Ƙananan Hukumomin Da Ke Fuskantar Barazanar Tsaro

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.