• English
  • Business News
Thursday, July 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus

by Sadiq
2 months ago
in Manyan Labarai
0
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Ondo Da Shugaban Masu Rinjaye Sun Yi Murabus
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Ondo, Abayomi Akinruntan, da Shugaban Masu Rinjaye, Emmanuel Ogunmolasuyi, sun sauka daga muƙamansu.

Akinruntan, ɗan sarkin Ugbo, Oba Frederick Obateru Akinruntan daga ƙaramar hukumar Ilaje, bai bayyana dalilin saukarsa ba.

  • Shehu Sani Ya Buƙaci Shugabannin Arewa Su Mara Wa Tinubu Baya Ya Yi Shekaru 8 A Kan Mulki
  • Bello Yabo Ya Je Wajen Wa’azi Da Bindiga A Sakkwato, Ya Ce Ya Shirya Kare Kansa

A cikin wasiƙar saukarsa, ya gode wa ‘yan majalisar bisa yadda suka zaɓe shi a matsayin mataimakin kakakin majalisar.

Kodayake ba a bayyana a hukumance dalilin saukarsa ba, wasu majiyoyi sun ce saukarsa na da nasaba da harkokin siyasa.

Wasu na ganin hakan na da alaƙa da kasancewarsa daga ƙaramar hukuma ɗata da Gwamna Lucky Aiyedatiwa.

Labarai Masu Nasaba

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya

Wasu kuma sun ce akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan da mahaifinsa, Oba Akinruntan.

Bayan saukar Akinruntan, an zaɓi Ololade Gbegudu daga Okitipupa a matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar.

Gbegudu, mai shekara 42, ya riƙe muƙamin shugaban kwamitin tsaro da ci gaban al’umma a majalisar kafin wannan sabon muƙamin.

Oluwatoyin James daga Akoko ta Arewa Maso Gabas ne, ya ayyana sunansa, yayin da Chris Aiyebusiwa daga Okitipupa I ya mara masa baya.

Haka kuma, tsohon jagoran majalisar, Ogunmolasuyi daga Owo I, ya sauya wajen aiki da Olatunji Oshati daga mazaɓar Ose, wanda yanzu shi ne sabon shugaban masu rinjaye.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: MurabusOndo
ShareTweetSendShare
Previous Post

Shehu Sani Ya Buƙaci Shugabannin Arewa Su Mara Wa Tinubu Baya Ya Yi Shekaru 8 A Kan Mulki

Next Post

Sin Da Masar Sun Cimma Yarjejeniyar Kafa Cibiyar Harkokin Kasuwanci Ta Sabon Birnin Masar 

Related

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP
Manyan Labarai

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

7 hours ago
Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya
Manyan Labarai

Tinubu Ya Tsawaita Wa’adin Shugaban Kwastan Da Shekara Ɗaya

8 hours ago
Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC
Manyan Labarai

Matsalar Tsaro: Tinubu Ya Ziyarci Jama’a, Ya Daina Sauraron Gwamnoni — ADC

14 hours ago
Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya
Manyan Labarai

Za A Kammala Aikin Titin Jirgin Ƙasan Kaduna-Kano A 2026 – Gwamnatin Tarayya

17 hours ago
Matatar Mai Ta Fatakwal Ba Ta Siyarwa Ba Ce – NNPC
Manyan Labarai

Matatar Mai Ta Fatakwal Ba Ta Siyarwa Ba Ce – NNPC

1 day ago
Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana
Manyan Labarai

Majalisar Dattawa Ta Yi Allah-wadai Da Zanga-zangar Ƙin Jinin ’Yan Nijeriya A Ghana

1 day ago
Next Post
Sin Da Masar Sun Cimma Yarjejeniyar Kafa Cibiyar Harkokin Kasuwanci Ta Sabon Birnin Masar 

Sin Da Masar Sun Cimma Yarjejeniyar Kafa Cibiyar Harkokin Kasuwanci Ta Sabon Birnin Masar 

LABARAI MASU NASABA

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

Mujallar Qiushi Za Ta Wallafi Jawabin Xi Jinping Game Da Kiyaye Muhallin Halittu

July 31, 2025
Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

Dangote Ya Bada Shawarar Samar Da Gidaje Masu Rahusa Da ‘Yan Nijeriya Za Su Iya Mallaka

July 31, 2025
NIN-SIM: Masu Hulda Da Kamfanonin Sadarwa Sun Koka Kan Katse Layinsu Daga Tsarin Kira

Kamfanonin Sadarwa Za Su Ci Gaba Da Rajistar Sabon SIM – NIMC

July 31, 2025
Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

Matsayar Bai Daya Da Sin Da Amurka Suka Cimma Ta Fuskar Haraji Na Da Babbar Ma’ana

July 31, 2025
Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

Mutane 44 Suka Mutu Bayan Mamakon Ruwa Da Aka Tafka A Beijing

July 31, 2025
Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

Yadda Yajin Aikin Ma’aikatan Jinya Ya Bar Baya Da Kura A Asibitocin Jihar Filato

July 31, 2025
Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

Zargin Da Wasu ’Yan Siyasar Amurka Ke Yi Wa Sin Na Fitar Da Hajoji Fiye Da Kima Ya Sabawa Hujjoji Na Hakika

July 31, 2025
Gwamnatin Borno Ta Nada Kwamitin Aiwatar Da Mafi Karancin Albashi

Gwamna Zulum Ya Sauke Kwamishinoni Biyu Tare Da Maye Gurbinsu Da Wasu

July 31, 2025
Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

Uganda Ta Jinjinawa Gudummawar Sin Ga Manufofin Wanzar Da Zaman Lafiya A Yankin Kahon Afirka

July 31, 2025
Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Yanzu-yanzu: Sanata Dino Melaye Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

July 31, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.