Mataimakin shugaban kasar Sin Han Zheng, ya gabatar da jawabin bude taron wanzar da zaman lafiya na kasa da kasa karo na 11, wanda ya gudana a jami’ar Tsinghua dake birnin Beijing a yau Lahadi, inda ya yi kira ga daukacin sassa da su ba da gudummawar wanzar da zaman lafiya da tsaro a duniya.
Han Zheng, ya ce Sin a shirye take ta yi aiki da sauran kasashe, wajen kare zaman lafiya da tsaro, da neman ci gaba da wadata, tana kuma yayata bukatar yin musaya, da koyi da juna tsakanin wayewar kan dukkanin bangarori, tare da raba moriyar ci gaban bil adama, da tsaro, da wayewar kai.
Daga nan sai ya jaddada cewa, zamanantar da kai irin na kasar Sin, na kan dogaro ne kan ci gaba cikin lumana, kuma har kullum Sin na nacewa manufofin ta na yayatawa, da gina zaman lafiyar duniya.
Taron na bana mai taken “daidata duniya mai tangal tangal ta hanyar cimma matsaya da hadin gwiwa”, ya kunshi kananan taruka 4, da dandaloli 19.
Ana kuma sa ran tattauna batutuwa da suka kunshi dabarun tsara sabon salon daidaita alakar Sin da Amurka, da wanzar da tsaro a yankin tekun Asiya da Fasifik, da ingiza amincewa juna tsakanin Sin da Turai, da samar da zaman lafiya a gabas ta tsakaniya, da bunkasa hadin gwiwar shawarar ziri daya da hanya daya. (Saminu Alhassan)