Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana jimaminsa bisa rasuwar tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya rasu yau Lahadi a birnin Landan yana da shekaru 82.
Wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Isma’il Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya bayyana marigayi Buhari a matsayin gwarzon da ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan Nijeriya.
- Tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari Ya Rasu A Landan
- Muhimman Abubuwa 10 Da Kowa Zai So Ya Sani Game Da Marigayi Shugaban Ƙasa Buhari
Ya ce, janaral Buhari, wanda ya shugabanci ƙasar nan a a mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1985, sannan kuma aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa na mulkin dimokuraɗiyya daga shekarar 2015 zuwa 2023, yana da hangen nesa na ci gaban ƙasa da samar da haɗin kai mai ɗorewa.
Sanata Barau ya ce, Buhari ba wai jigo ne kawai a tarihin Nijeriya ba, har ma yadda ya gudanar da rayuwarsa kan haƙuri da ƙaunar ƙasa, inda ya sadaukar da kansa wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro da ma ci gaban ƙasar nan.
Barau Ya miƙa ta’aziyyarsa ga mai daƙin marigayin, Haj. Aisha Buhari da ’ya’yansa da sauran danginsa, yana roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da ya ba su ƙarfin hali da juriyar wannan babban rashi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp