A yayin taron manema labarai da ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar kasar Sin ta shirya a yau, wani dan jarida ya yi tambayar cewa: “Ta yaya hukumar kwastam ta kasar Sin ke duba tasirin karin harajin da Amurka da Sin suka sanyawa juna, wanda zai fara aiki tun daga gobe Talata 14 ga watan nan, kan jiragen ruwa da ke shiga tasoshin ruwa, ga cinikin shige da fice na Sin?”
Game da wannan tambaya, kakakin hukumar kwastam ta kasar Sin Mr. Lv Daliang ya ce, game da batun karbar karin haraji kan jiragen ruwa da suke tsayawa a tasoshin ruwa, hukumomi da dama sun riga sun yi magana a baya, kuma matakin da Amurka ta dauka na nuna son kai ne da bangaranci. Ya kara da cewa, matakan da Sin ta dauka na mai da martani sun zama wajibi, kuma matakan tsaro ne da ba za a iya kaucewa ba, don kare hakkin masana’antu da kamfanoninta, da kuma tabbatar da yanayin gasa mai adalci a kasuwannin jigilar kayayyaki, da na gina jiragen ruwa na duniya.
Jami’in ya kuma yi fatan Amurka za ta fahimci kuskuren da ta yi, ta kuma dauki matakin da ya dace na bin hanya daya tare da Sin, don yin hadin gwiwa, tare da komawa kan hanyar tattaunawa da sassantawa. (Amina Xu)