A duk yayin da mace ta tabbatar tana dauke da ciki, abu uku ya kyautu ta yi dangane da rikafin masu ciki.
Da farko za ta samo ganyen na’a-na’a da garin habbatussauda da kuma zuma.
- Tsadar Rayuwa Ba Zai Sa Tinubu Ya Yi Murabus Ba: Martanin Gwamnatin Tarayya Ga Gwamnonin PDP
- Yadda Zaki Ya Halaka Mai Ba Shi Abinci Har Lahira
Idan wannan bai samu ba, sai a samu man zaitun da man habbatussauda, a hada su wuri guda; kowannensu ya kasance kamar rabin lita ko lita guda, sannan a tabbata an samu masu kyau ba jabu ba.
A kullum, bayan garin Allah ya waye, sai ta sha cokali daya na wannan mai na habba da zaitun da zuma kafin ta ci komai, haka nan da rana ma za ta sha cokali daya.
Bayan cikin ya kai wata uku zuwa shida, sai ta koma shan cokali biyu da safe, biyu da rana, biyu da dare. Haka zalika, daga lokacin da cikin ya kai wata bakwai zuwa wata tara, sai ta koma shan cokali uku da safe, uku da rana, uku da dare.
Haka nan, daga lokacin da ta zo daf da haihuwa, sai ta koma cin danyen dabino guda uku ko bakwai ko kuma tara akalla sau uku a wuni.
Hikimar yin hakan a nan ita ce; danyen dabino zai yi saurin kawo mata ruwan nono, sannan zai taimaka wajen saurin fitar da jinin da ya daskare a mararta. Idan kuma so samu ne, ta fara cin wannan danyen dabino tun saura wata guda kafin lokacin haihuwarta ta ya kama.
Haka zalika, bayan cin wannan danyen dabino; ana so wannan mai ciki ta dawwama a kan shan ruwan zafi wanda aka tafasa da ganyen na’a-na’a da zuma da kuma garin habbatussauda, domin kuwa yana matukar saukaka mata wajen fitar da jariri.