Wani rahoto kan ci gaban wayewar kan intanet ya nuna cewa, kasar Sin ta cimma nasarori wajen daidaita harkokin intanet ta hanyar kaddamar da managartan matakan daidaita yadda ake amfani da intanet yadda ya kamata, da inganta mu’amala da hadin gwiwar kasa da kasa a tsarin amfani da intanet.
Rahoton kan ci gaban wayewar kan intanet na kasar Sin na shekarar 2023, wanda aka fitar Talatar nan, a yayin taron wayewar kan intanet na shekarar 2023 da ake ci gaba da yi a birnin Xiamen na kudu maso gabashin kasar Sin, ya bayyana cewa, an ci gaba da inganta hanyoyin da ake ba da rahoto da magance yada jita-jita ta yanar gizo, da samar da yanayi mai kyau ga jama’a game da tsarin amfani da kafar intanet. (Mai fassara: Ibrahim)