• English
  • Business News
Friday, October 31, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matar Aure Ta Hallaka Mijinta A Bauchi Kan Shirin Kara Aure

by Khalid Idris Doya
2 years ago
Bauchi

Wata mata mai suna Maimunatu Sulaiman ‘yar shekara 21 a duniya da ke zaune a unguwar Kofar Dumi a kwaryar Bauchi ta kashe mijinta, Aliyu Mohammad sakamakon rashin jituwar da ta barke a tsakaninsu.

Majiya daga yankin ta bayyana cewa an samu rashin jituwa ne a tsakanin miji da matar ne sakamakon yunkurin da mijin ya yi na kara aure.

  • Ina Son Kara Aure, Ko Me Yake Kawo Matsaloli Tsakanin Kishiyoyi Da Yadda Za A Magance?
  • Batun Sake Sulhu Da ‘Yan Bindiga A Sikeli

Kazalika, an ruwaito cewar matar ta daddaba wa mijin wuka ne a kirjinsa wanda hakan ya yi sanadin ajalinsa.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 5 ga watan Yulin 2023 a unguwar Kofar Dumi.

Rundunar ‘yansandan Jihar, ta ce kawo yanzu sun cafke matar da ake zargi da kisan kan.

LABARAI MASU NASABA

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

Sanarwar da kakakin ‘yansandan jihar, ASP Aminu Gimba Ahmed ya fitar a ranar Juma’a ta ce, “A ranar 5 ga watan Yuli 2023 jami’an caji ofis din ‘yansanda da ke Township, Bauchi sun kama wata Maimunatu Sulaiman kan zargin aikata kisan kai.

“Lokacin da jami’an suka samu rahoton faruwar lamarin, sun garzaya zuwa inda lamarin ya faru tare da daukar wanda lamarin ya ratsu da shi da ita kanta wadda ake zargi zuwa asibitin koyarwa na Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi.

“Amma likitoci sun tabbatar da mutuwar mijin sakamakon rauni da ya samu a kirjinsa, yayin da ita kuma wadda ake zargin ta samu wasu raunuka a cikinta.”

Binciken ‘yansanda ya nuna cewa wadda ake zargin ta soki mijinta a kirjinsa sakamakon rashin jituwar da ta barke a tsakaninsu.

Wadda ake zargin ta amsa laifin da ake tuhumarta da shi.

Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Auwal Musa Mohammad, ya umarci mayar da binciken lamarin zuwa sashen kula da manyan laifuka (SCID) don zurfafa bincike.

Ya ce za a gurfanar da wadda ake zargin da zarar an kammala bincike.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa
Labarai

Ƴansanda Sun Kama  Wani Mai Wasa Da Bindiga AK-47 A Cikin Wani Bidiyo A Adamawa

October 31, 2025
Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar
Manyan Labarai

Kifewar Kwalekwale: Gwamnan Gombe Ya Jajanta Wa Al’ummar Nafada Kan Mutuwar Matasa Biyar

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP
Manyan Labarai

NPA Da Ƙungiyar Injiniyoyi Ta Yi Haɗaka Don Bunƙasa Tashoshin Jiragen Ruwa

October 31, 2025
Next Post
‘Muhallin Mutum 43,000 Aka Cunkusa Alhazan Nijeriya 95,000 A Mina’

Ranar Foliyo Ta Duniya: Muna Fatan Ganin Karshen Cutar Foliyo A Jihar Katsina -Zulaihat Dikko Radda

October 31, 2025
Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

Yan Nijeriya Na Ɗanɗana Kuɗarsu Kan Jinkirta Cire Tallafin Mai – Sarki Sanusi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Allah Ya Kai Manzon Allah (SAW) Muƙami Na Babban Yabo A Cikin Komai

October 31, 2025
Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

Sin Da Amurka Suna Taimaka Wa Juna Da Samun Wadata Tare

October 31, 2025
Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

Xi Jinping Ya Halarci Kwarya-Kwaryan Taron Shugabannin APEC Na 32 Tare Da Gabatar Da Jawabi

October 31, 2025
Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

Musabbabin Hana Sule Lamido Fom Ɗin Takarar Shugabancin PDP

October 31, 2025
Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

Matsalar Talauci Da Rashin Tsawon Rai Da ‘Yan Nijeriya Ke Fuskanta

October 31, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.