Wata matar aure mai suna Fatima Mohammed, ‘yar shekara 28 a duniya tana fuskantar zargi da tuhumar kashe kishiyarta, mai suna Hajara Isa, ‘yar shekara 20 a duniya a unguwar Sarakuna da ke cikin garin Bauchi.
Abun takaicin na mutuwar Hajara Isa ya faru ne a gidan aurenta a ranar 28 ga watan Fabrairun 2025.
- A Otal Ya Mutu Ba ‘Yan Fashi Ne Suka Kashe Tsohon Kwanturolan NIS Ba – ‘Yansanda
- Kotu Ta Ɗaure ‘Yan Tiktok 2 Kan Yaɗa Kalaman Batsa A Kano
LEADERSHIP Hausa ta labarto cewa a ‘yan kwanakin nan ana yawan samun rahoton kisan gilla a Bauchi lamarin da ke buƙatar masu ruwa da tsaki su maida hankali a kai domin ɗaukan matakan gaggawa.
A sanarwar da ‘yansanda suka fitar na cewa, “A ranar 3 ga watan Maris, 2025 wani mutum mai suna Sale Isa da ke unguwar Sarakuna a cikin garin Bauchi ya kai rahoto ga jami’an ‘yansanda dangane da rasuwar Hajara wacce iyalai suka yi nuni da cewa, akwai yiwuwar kishiyarta na da hannu a lamarin.”
Sanarwar da jami’in watsa labarai na hukumar ‘yansanda jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil ya fitar a ranar Laraba, ya ce, a halin yanzu rundunar ta duƙufa wajen gudanar da cikakken bincike kan lamarin kisan.
Tunin Kwamishinan ‘yansandan jihar Bauchi, CP Auwal Musa Muhammad ya umarci babban baturen ɗansanda a C Division da ya jagoranci tawaga ta musamman da za su gudanar da bincike kan lamarin a tsanake.
A cewar jami’in hulda da jama’a na rundunar, yunkurinsu a halin yanzu ya kai ga kama Fatima Mohammed, kishiya ga mamaciyar wacce a halin yanzu take tsare a hannunsu.
“Bincike na farko ya nuna cewa, akwai zargin Fatima Mohammed na da hannu a mutuwar Hajara. A yayin da ake yi mata tambayoyi, an ce ta amince ta shaƙe ta har lahira, sannan ta yi yunƙurin ɓoye laifin ta hanyar zuba mata tafasasshen ruwa tare da ƙona jikinta da buhun da ke narkewa,” in ji CSP Wakil
A sanarwar, rundunar ‘yansandan jihar Bauchi ta tabbatar da aniyarta na wanzar da adalci a kowani lokaci, inda ta ce za a mayar da kes ɗin zuwa sashin kula da manyan laifuka SCID.
Wakil ya ƙara da cewa Kwamishinan ‘yansandan jihar ya umarci tawagar kwararru da su hanzarta tattara bayanan da suka shafi wannan mutuwar ciki har da zarge-zarge da ake yi kan mutuwar Hajaran.
CP Auwal ya hori jama’an binciken da su gaggauta gudanar da bincike su tare da aiki da kwarewa inda ya tabbatar da cewa za su yi ƙoƙarin wanzar da adalci.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp