Matar Gwamnan Jihar Kebbi, Hajiya Nafisa Nasir Idris ta raba kayayyakin tsaftar Jinin Al’ada (Haila) ga dalibai tare da bayar da gudunmuwar Naira miliyan daya ga daliban da suka kammala rubuta jarrabawar makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Argungu.
An gudanar da bikin ranar tsaftar Jinin Al’ada na duniya ne a makarantar sakandaren da ke Argungu a karshen makon nan da muke ciki.
- Matsalolin Gidan Aure (4) Mijina Ba Ya Kula ‘Ya`yana
- ‘Yan Ta’adda Sun Kakaba Harajin N100,000 Ga Kowane Manomi A Wasu Yankunan Kaduna
Bikin na ranar 28 ga watan Mayu ya kasance ranar tsaftace ta Jinin al’ada na duniya karo na 10, wani shiri na duniya da aka sadaukar domin wayar da kan dalibai mata game da tsaftar jinin al’ada a makarantu da gidajensu.
Hajiya Nafisa, ta yabawa maigidanta Gwamna Nasir Idris bisa tallafin da yake bayarwa a fannin kiwon lafiya da kuma kokarin da yake yi na inganta tsaftar jinin al’ada a jihar.
A nasu jawabin, kwamishiniyar harkokin mata ta jihar, Hajiya Halima Hassan-Kamba da uwargidan sakataren gwamnatin jihar (SSG), Hajiya Asma’u Alkali, sun bukaci daliban da su kasance jakadu nagari ga iyayensu da malamansu da sauran al’umma a zamansu na rayuwa.
A fadar Sarkin Argungu, Mai martaba Sarkin Kabin Argungu, Alhaji Samaila Muhammad-Mera, ya yaba wa matar Gwamnan bisa goyon baya da gudunwa da ta bayar na tabbatar da yakin wayar da Kan ‘ya’ya mata da sauran al’umma kan tsaftar jinin al’ada a tsakanin jinsin mata a fadin jihar.