Wata mata mai suna Laraba da ke zaune a jihar Adamawa ta tona asiri, kan yadda ta rasa ‘ya’yanta guda hudu a jihar Adamawa da mijinta mai suna Elisha Tari, wanda ya tabbatar da cewa shi ya kashe guda biyu daga cikin ‘ya’yan nasa hudu da aka kashe Elisha wanda a yanzu haka yana garkame a wajen ‘yansanda, ya bayyana wa manema labarai yadda wani mutum ya buga wa ‘ya’yansa guda biyu dutse aka, har suka mutu.
Elisha dai dan asalin kauyen Himike ne da ke karamar hukumar Michika, kuma an samu nasarar kama shi, bayan da aka sanar da ‘yansanda ya kashe ‘ya’yansa guda biyu, ta hanyar buga musu dutse.
- Jami’an Kashe Gobara Sun Ceto Mutum 91 Da Dukiyar Da Ta Kai Kusan Naira Miliyan 25 A Kano
- A KUSKURA: Yadda Kayan Maye Ya Zama Ruwan Dare A Tsakanin Al’umma
Matar ta sa mai suna Laraba ta tsallake rijiya da baya daga hannun mijin nata bayan ya yi yunkurin kashe ta.
A tattaunawar Laraba, da ‘yanjarida ta ce, tana da ‘ya’ya hudu ta kuma yi bari sau daya tare da Elisha, amma biyun daga cikin ‘ya’yan sun mutu su kuma ragowar biyun ubansu ne ya kashe su.
Ta ce mijin nata yana shan wiwi da giya da tiramol kuma yana yin shake, ya zo bayan ta samu ‘ya’ya ya kashe su. Ta ce tana shan matukar wahala a hannunsa.