Wani gwanin iya magana ya ce: Kwanaki mafi dadin dadadawa na rayuwa su ne kwanakin da na yi da matar wani, mahalarta taro suka yi shiru cike da mamaki ,sai ya kara da cewa ita ce mahaifiyata.
Taro ya kaure da ihu da kuma tafi. Wani da ya halarci taron sai ya kudiri niyyar yi wa matarsa wannan barkwancin a gida, bayan sun kammala cin abinci sai ya ce da matarsa kwanaki mafi dadin dadadawa na rayuwa su ne,
kwanakin da na yi da matar wani, bayan wani lokaci sai ya fara kokarin tuno ci gaban maganar, lokacin da ya dawo hayyacinsa sai ya samu kansan a gadon Asibiti, yana jinyar mummunar kunar da ya samu sakamakon zazzafan kishin matarsa, ta kwarara masa tafasheshen ruwan zafi.