Matasa biyar sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a Kogin Nafada da ke karamar hukumar Nafada ta jihar Gombe.
Wannan mummunan lamari ya faru ne a ranar Asabar lokacin da wani jirgin ruwa da ke jigilar fasinjoji zuwa kasuwar kauye ya kife, inda ya dulmiyar da fasinjojin cikin ruwan.
An tsamo gawarwakin wadanda lamarin ya rutsa da su, da suka hada da Najib Ibrahim (18), Hauwa’u Jidda Adamu Siddi Dogal (15), Ummati Haruna Baraya (16), Umaira Gidado (16), da Amina Jaliya (15).
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana matukar bakin ciki game da wannan lamarin.
Gwamnan, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Ismaila Uba Misilli ya fitar, ya yi ta’aziyya ga iyalan da suka rasu da kuma dukkan al’ummar Nafada, yana addu’ar Allah ya jikan mamatan.














