Wasu matasa sun daka wawa kan kayan tallafin watan Ramadan da aka ce Seyi Tinubu dan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne zai raba a jihar Gombe.
In ba a manta ba, a ‘yan kwanakin nan, Seyi Tinubu ya kai ziyara jihohin Arewa inda ya ke tare da jama’a da shugabannin siyasa domin buda baki da su.
- Mataimakin Firaministan Kasar Sin Ya Karfafa Gwiwar Kamfanonin Kasashen Duniya Da Su Fadada Zuba Jari A Sin
- Yaushe Ronaldo Zai Daina Jefa Kwallo A Raga?
A irin wannan ziyarce-ziyarcen, dan shugaban kasa ya kan kaddamar da shirin ciyar da masu karamin karfi a watan Ramadan.
Shirin ya fuskanci suka sosai a shafukan sada zumunta, inda suke ganin cewa, Arewa ta cancanci kulawa fiye da haka, yayin da wasu kuma ke ganin tallafin ya dace.
A wani faifan bidiyo da Daily Trust ta gani, an ga wasu fusatattun matasa suna kwashe kayan abinci a wata babbar mota da aka ajiye a bakin titi.
An ga matasan suna jefo kayan ga wadanda suke kasa domin tattarawa musu, sannan suka yi awon gaba da kayayyakin.
Abubuwan da ke cikin Tirelar sun haɗa da shinkafa, sukari, man girki, gishiri da taliya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp