Wasu ƙungiyoyin matasa daga yankin Kwara ta Kudu sun yi kira ga gwamnati da ta gaggauta tura dakarun Sojoji masu yawa domin kawar da ƴan bindiga da suka addabi al’ummominsu tare da dawo da zaman lafiya.
Wannan kira ya fito ne daga shugabannin ƙungiyoyin Igbomina Youth Assembly (IYAss), da Kwara South Youth Development Organisation (KWAYORG), da Kwara South Consultative Youth Forum (KSCYE) da sauran ƙungiyoyin matasa na yankin a wani taron manema labarai da aka gudanar a Igbomina House, Ganmo.
- Kwararre Ya Ja Hankali Kan Sayar Da Takin Zamani Da Ba A Tantace Shi Ba
- ‘Yan Nijeriya Miliyan 40 Ke Fuskantar Barazanar Kwararowar Hamada – Ministan Muhalli
Shugaban IYAss, Injiniya Ajibola Olugbenga, wanda shi ne mai magana da yawun ƙungiyoyin, ya ce abin da ake buƙata shi ne kafa cikakken sansanin Soja a yankin, ba wai zuwan sintiri na lokaci-lokaci kaɗai ba. Ya kuma jaddada muhimmancin gudanar da aiyukan tsaro cikin gaggawa, da sa ido ta sama, da kuma lalubo dazuzzukan da ƴan ta’adda ke ɓuya, tare da samar da makamai na zamani da kayan aiki ga mafarauta da masu sa-kai da ke zama garkuwar farko ga jama’a.
Olugbenga ya kuma yi kira da a kafa dokar ta-baci na awanni 12 (daga ƙarfe 6 na yamma zuwa 6 na safe) a garuruwan da lamarin ya fi kamari, domin bai wa sojoji damar gudanar da aikin share ƴan ta’adda. Haka kuma ya nemi kafa rundunar haɗin gwuiwar tsaro da za ta haɗa jami’an tsaro na tarayya, da jiha, da ƙananan hukumomi tare da wakilan matasa don tabbatar da aiki da gaskiya.
Shugaban KWAYORG, Prince Abolarin Sharafa, ya kuma buƙaci wakilan majalisar dokoki da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa daga yankin su haɗa kai da gwamnati domin tabbatar da an kawar da ƴan ta’adda daga ƙauyukan. Ya ce, “Muna buƙatar Sojoji, muna buƙatar tsauraran matakan tsaro, muna buƙatar kariya ga rayukan al’ummarmu. Barazana ga Kwara ta Kudu barazana ce ga Nijeriya baki ɗaya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp