Matatar man Dangote ta sanar da dakatar da sayar da man fetur a naira.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da matatar ta aika wa abokan huldarta a yammacin ranar Laraba.
- ‘Yan Bindiga Sun Sace Mutum 7 A Jihar Neja
- El-Rufai Ya Shiga Tsilla-tsilla Bayan Rasa Kujerar Minista – APC
A cikin sanarwar, Matatar ta ce, wannan matakin na wucin gadi ne, inda ta bayyana dalilin da ya sa aka dauki matakin domin samar da daidaito tsakanin farashin danyen mai da aka siyo da Dala da kuma na Naira.
“Muna so mu sanar da ku cewa, matatar man Dangote ta dakatar da sayar da man fetur a Naira na wani dan lokaci domin kauce wa rashin daidaito tsakanin danyen man da ke wurinmu wanda a halin yanzu ke kan farashin dalar Amurka.
“Ya zuwa yanzu, cinikin man fetur da muke samu a Naira ya zarce na danyen man da muka samu a farashin Naira, a sakamakon haka, dole ne mu daidaita kasuwancinmu na dan lokaci.
“Muna ci gaba da jajircewa wajen ci gaba da bai wa ‘yan kasuwannin Nijeriya kayayyakinmu mai inganci da zarar mun samu danyen man fetur daga kamfanin NNPC, nan take za mu dawo da cinikin man fetur a Naira”.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp