Matatar Dangote ta sake rage farashin man fetur zuwa Naira 835 kan kowace lita.
Sabon farashin a matatar mai yanzu shi ne Naira 835 kan kowace lita, daga tsohon farashin da yake a Naira 865.
- UEFA: Mbappe Zai Jagoranci Real Madrid Yayin Da Ta Ke Fatan Kafa Sabon Tarihi A Santiago
- Ina Da Ƙwarewar Da Zan Iya Zama Shugaban Ƙasar Nijeriya – Makinde
Rage farashin ya biyo bayan faɗuwar farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya, inda farashin ya sauka zuwa dala 64 kan kowace ganga, daga sama da dala 70 a makonnin da suka gabata.
A baya ma, matatar ta rage farashin daga Naira 880 zuwa Naira 865, amma yawancin masu sayar da mai ba su rage farashin ga masu saye ba.
Matatar mai ta Dangote na ɗaya daga cikin manyan matatun mai a Nijeriya, wadda ta ke da ƙarfin tace gangar ɗanyen mai 650,000 a kowace rana.
Ƙarin bayani na tafe…
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp