Matatar mai ta Haifa, wadda ke ƙarƙashin babban kamfanin sarrafa mai na ƙasar Isra’ila, ta dakatar da dukkanin ayyukanta bayan wani harin makami mai linzami da Iran ta kai a yankin.
Kamfanin ya bayyana cewa, ko da yake harin bai jikkata ma’aikata ko wasu da ke kusa da matatar ba, sai dai sun yanke shawarar dakatar da ayyuka nan take domin kare lafiyar mutane da kuma tsaftar muhalli.
- Dalilin Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare da Ambaton Shettima Ba – Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas
- ‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano
Matatar Haifa na ɗaya daga cikin manyan cibiyoyin samar da makamashi da Isra’ila ke dogaro da su.
Wannan lamari na zuwa ne a wani lokaci da ake ci gaba da samun rashin jituwa tsakanin Iran da Isra’ila, abin da ke barazana ga tsaron makamashi da sauran ababen more rayuwa a yankin.
Masana harkokin tsaro da tattalin arziƙi sun bayyana cewa irin waɗannan hare-hare na iya shafar tsadar mai da kuma kawo tangard5a ga masana’antu da zirga-zirgar ababen hawa a ƙasar.
Hukumomin Isra’ila na ci gaba da bincike tare da ɗaukar matakan gaggawa domin daƙile tasirin harin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp