ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Wednesday, September 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Dalilin Mara Wa Tinubu Baya Ba Tare da Ambaton Shettima Ba – Shugaban APC Na Arewa Maso Gabas

by Sadiq
1 year ago
Shettima

Mataimakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa mai kula da yankin Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu, ya bayyana dalilin da ya sa ya mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin sake tsayawa takara a 2027 ba tare da ambaton Mataimakin Shugaba Ƙasa, Kashim Shettima, a jawabinsa ba. 

Jawabin nasa ya janyo ce-ce-ku-ce a taron shugabannin APC na Arewa maso Gabas da aka yi a Jihar Gombe.

  • ‘Yansanda Sun Kama Matasa 51 da Ake Zargi Da Faɗan Daba A Kano
  • Sabon Shirin Gwamnatin Katsina: Za A Fara Sauya Tunanin Tubabbun ‘Yan Bindiga

Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels, Salihu ya ce ba a fahimce shi ba ne, kuma kafafen yaɗa labarai sun bayar da rahoton ba daidai ba.

ADVERTISEMENT

“Wannan matsala ta faru ne saboda yadda aka yi wa jawabina fassara ba daidai ba. Da an saurari jawabin gaba ɗaya, musamman ƙarshensa, da an ji na yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙasa,” in ji shi.

Salihu ya ce kafin ya nemi a goyi bayan Tinubu ya sake tsayawa takara, ya fara da yaba wa Shettima da sauran ‘yan yankin Arewa maso Gabas da aka ba su manyan muƙamai a gwamnati.

LABARAI MASU NASABA

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

“Na ce Shettima ɗanmu ne, kuma muna alfahari da shi. Na kuma gode wa Tinubu bisa yadda ya bai wa ‘yan Arewa maso Gabas muƙamai masu gwaɓi kafin na nemi a mara masa baya,” in ji Salihu.

A lokacin taron, wasu matasa sun kusan kai masa hari, amma ya ce hakan ya faru ne saboda wasu ba su fahimci abin da ya yi ba.

Ya kuma jaddada cewa a tsarin jam’iyya, mutum ɗaya ne kawai ake zaɓa a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa a lokacin zaɓen fidda gwani, kuma shi ne ke da ‘yancin zaɓar mataimakinsa.

“Ba a daidaita tikitin shugaba da mataimaki a zaɓen fidda gwani. Ɗan takara kawai ake zaɓa, kuma yana da ‘yancin zaɓar wanda zai mara masa baya,” in ji shi.

Salihu ya kuma ƙaryata jita-jitar cewa akwai saɓani tsakanin Tinubu da Shettima.

Ya zargi wasu da ya kira “’yan kasuwar rikici” da ƙoƙarin ɓata lamarin domin amfanin kansu.

“Waɗanda ke yaɗa irin waɗannan labarai suna neman cin moriyar rikicin ne. Ba a gudanar da harkokin jam’iyya a dandalin sada zumunta ko a jaridu ba, a ofishin jam’iyya ake yin hakan,” in ji shi.

A ƙarshe, Salihu ya roƙi mambobin jam’iyyar da al’umma su guji yarda da jita-jita, yana mai cewa jam’iyyar APC na nan daram, babu wata matsala.

MASU ALAKA

Sojoji
Manyan Labarai

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027
Siyasa

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Ballon D'or
Manyan Labarai

Ballon d’Or: Messi, Yamal, Da Mane Na Cikin ‘Yan Wasa 30 Da Aka Zaɓo

September 8, 2026
Next Post
Matatar Mai ta Haifa Ta Dakatar Da Ayyukanta Bayan Harin Iran

Matatar Mai ta Haifa Ta Dakatar Da Ayyukanta Bayan Harin Iran

LABARAI MASU NASABA

Taron PDP Na Ƙasa: Ɓangaren Wike Ya Kafa Sabon NWC A Abuja

PDP Ta Musanta Mara Wa APM Baya A Bauchi

September 9, 2026
Sojoji

Sojoji Sun Dakile Hare-Hare, Sun Ceto Mutane 12 A Zamfara

September 9, 2026
Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

Batun AI Zai Fi Daukar Hankali A Bikin Baje Kolin Fasahar Zamani Ta Duniya Karo Na 5

September 8, 2026
Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

Gwamna Radda Ya Samu Goyon Bayan APC A Katsina Gabanin Zaɓen 2027

September 8, 2026
Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

Cinikin Wajen Sin Ya Ci Gaba Da Samun Bunkasa Cikin Sauri A Watanni Takwas Na Farkon Bana

September 8, 2026
'Yan Bindiga

‘Yan Bindiga Sun Kashe 2, Sun Yi Garkuwa Da 26 A Kaduna

September 8, 2026
Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

Binciken CGTN Ya Nuna Gamsuwa Da Yadda Baje Kolin CIFTIS Ke Shaida Karfin Gwiwar Sin A Fannin Kara Fadada Bude Kofa Bisa Babban Matsayi

September 8, 2026
Yadda Taron Tattalin Arziki Da Zuba Jari Na Kwana Biyu Ya Gudana A Katsina

Gwamna Radda Ya Gabatar Da Kasafin N828.6bn Na 2027

September 8, 2026
Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

Sin Za Ta Yi Aiki Tare Da Sassa Daban Daban Domin Mayar Da Fasahar AI Wata Dama Ta Cin Gajiya Mai Dorewa

September 8, 2026
Gwamnan Kebbi Ya Bayyana Shirin Sake Duba Albashin Malaman Firamare

Gwamna Idris Ya Rushe Majalisar Shugabannin Hukumar Zaɓe Ta Kebbi

September 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.