Kamfanin Mai na Nijeriya (NNPCL), ya sanar da cewa matatar mai ta Warri, mai ƙarfin tace ganga dubu 125 a kullum, ta dawo aiki bayan an kammala gyare-gyare.
Shugaban kamfanin NNPCL, Mele Kyari, ya tabbatar da hakan yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai tare da tawagarsa a ranar Litinin.
- Ɓarayin Wutar Sola Sun Baƙunci Lahira Yayin Da Suke Tsaka Da Kwancewa
- Kasar Sin Ta Fitar Da Rahoton Farko Kan Bincike Da Aikace-Aikacen Tashar Sararin Samaniya
Ya ce, duk da cewa ba a kai ga dawo da matatar aiki ɗari bisa ɗari ba, an kusa cimma wannan matsayi.
“Mun kawo ku nan don ku gani da idonku cewa matatar ta fara aiki, duk da mutane da dama suna tunanin hakan ba zai yiwu ba,” in ji Kyari.
An gina matatar ta Warri tun a shekarar 1978, kuma NNPCL ke kula da ita.
Matatar na da muhimmanci sosai wajen samar da mai ga kudancin Nijeriya da kudu maso yamma.
Kyari, ya kuma jaddada cewa matatar na cikin wani tsari na gyare-gyare da zai tabbatar da cikakken aiki nan gaba.
Wannan shi ne wani mataki na ƙara samar da mai a cikin gida don rage dogaro da shigo da mai daga waje.