Matatar mai ta Dangote ta sanar da kara rage farashin dizel daga Naira 1,200 zuwa Naira 1,000 kan kowace lita a Nijeriya.
A makonnin da suka gabata, lokacin da matatar ta soma aiki, kamfanin yana sayar da farashin dizel a kan Naira 1,200 duk lita daya
- Kotu Ta Tabbatar Da Dakatar Da Ganduje Daga Shugabancin APC
- Idan Isra’ila Ta Kai Wa Iran Hari Ba Za Mu Goya Mata Baya Ba – Amurka
Hakan na nufin an yi ragin fiye da kashi 30 cikin 100 daga farashin da ake sayar da dizel din a baya kimanin Naira 1,600 kan kowace lita.
Matatar ta ce muhimmin ragin da aka yi kan farashin na dizel zai yi tasiri sosai a bangaren tattalin arziki tare da rage hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.
Matatar Dangote ta soma gudanar da harkokinta ne da sayar da man jirgi da kuma na dizel.
A gefe guda kuma dalar Amurka da ake alakanta da hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, na ci gaba da karyewa, inda darajar Naira ke ci gaba da tashi.