An kaddamar da babban taron raya sana’ar manhajojin na’urori masu kwakwalwa na kasa da kasa na kasar Sin, a jiya Talata 18 ga watan nan, inda jami’in ma’aikatar sadarwar masana’antun kasar Sin ya bayyana cewa, tun bayan babban taron wakilan JKS karo na 18, wanda aka kira a shekarar 2012, sana’ar manhajojin na’urori masu kwakwalwa na kasar ta samu bunkasuwa cikin sauri, inda aka rika sabunta muhimman fasahohin da suka danganci hakan, kuma matsakaiciyar karuwar saurin ci gaban sana’ar a ko wace shekara ya kai kaso 16 bisa dari.
Alkaluman kididdigar ma’aikatar sun kuma nuna cewa, adadin kudin shigar sana’ar ya zarce kudin Sin yuan triliyan 10 a shekarar 2022, adadin da ya karu da kaso 11.2 bisa dari kan na makamancin lokaci na shekarar 2021, kana ya dara adadin karuwar GDPn kasar a bara da kaso 8.2 bisa dari.
Jami’in ya kara da cewa, ma’aikatar sadarwar masana’antun kasar Sin za ta hanzarta nazarin muhimman fasahohin manhajoji, domin ciyar da sana’ar gaba yadda ya kamata. (Mai fassarawa: Jamila)