Hukuma mai kula da ikon mallakar fasaha ta kasar Sin, ta kira wani taron manema labarai a yau Litinin, inda ta bayyana cewa, ya zuwa karshen watan Nuwamba, yawan kamfanoni dake mallakar sabuwar lambar kira sun kai kashi 73.5%, na dukkan lambar kira mai daraja a nan kasar Sin, adadin da ya karu da kashi 2.5% bisa na makamancin lokacin bara.
Alkaluman sun nuna cewa, matsakaita da kananan kamfanonin Sin, na nuna himma da gwazo wajen kirkire-kirkire, da samun sabuwar lambar kira, kana karfinsu na kara karuwa a fannin kare ikonsu, da aiwatar da fasahohinsu. A shekarar bana, yawan lambar kira da aka yi amfani da su da wadannan kamfanoni suka samu sun kai 55.1%, wanda ya karu da kashi 3.6% bisa na makamancin lokacin bara. Daga cikinsu, wannan adadi ya kai kashi 57.8%, da 36.7%, a kanana da mafiya kankantar kamfanoni. (Amina Xu)