• English
  • Business News
Tuesday, October 28, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Al’ada Da Ciwon Mara Ga Mata

by Bilkisu Tijjani
2 months ago
Ciwon

Kamar yadda muka sani, mata kan fiskanci matasaloli daban-daban yayin zuwan al’ada ta zubar jini ko kuma wani farin ruwa daban.

Ciwon mara a yayin al’ada kan faru ne yayin da mahaifa ke curewa da motsawa waje guda domin fitar da wani abu daga cikinta marar amfani wanda wannan motsin shi ke sanya ciwon mara.

  • 2027: ‘Yan Siyasa Sun Yi Watsi Da Gargadin INEC, Sun Ci Gaba Da Yakin Neman Zabe
  • Sin Ta Samu Karin Kamfanoni Kusan Miliyan 20 A Cikin Shirin Shekaru Biyar Karo Na 14

A lura cewa akwai ire-iren abubuwa da kan zuba daga al’aurar mata kamar jini ko mai hade da ruwa ruwa, farin ruwa, ruwa mai kauri, ruwa mai wata kala daban, da sauransu, wanda hakan kan faru ne saboda wata matsala ta shigar kwayoyin cuta, ko dai ta birus, yeast infection, shan kwayoyin hana daukar ciki, saduwa barkatai, ciwon suga, cancer, shan barasa da sauransu. Idan an ga haka sai a gaggauta duwa ga likita. Wani lokaci al’ada kan rikice ko tsallake ba kuma tare da shigar ciki ba.

Zubar jinin haila ko wankin kamara yadda ake fada, kowace mace na da nata mataki daban wanda kan afka musu kafin saukar jinin a kowane wata. Wannan jini kan sauko ne daga mahaifa wanda kuma da zarar ya dauke an fi daukar ciki musammam kwanaki hudu ko biyar na farko. Zai fi kyau a lura da zuwan lokacin al’ada da adadin yawan jinin da yawan kwanakin da ya dace wadda idan har ya yi nisa shi ne kwana shida amma ga ‘yan mata yara ba ya wuce kwana daya zuwa biyu.

Idan ana fama da ciwo yayin al’ada ko lokacin karatowar al’ada, ko fama da ciwon mara, ciki, rashin walwala, kin cin abinci, kasala, nauyin jiki, tashin zuciya. To a lura cewa, akwai matakai da ya kamata abi don samun sassauci kamar:

LABARAI MASU NASABA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

Hadin Tsumin Baure

1. Sanin alamomin zuwan jinin kafin ya sauka, hakan kan taimaka wajen tsara al’amuran yau da kullum da rage wa kai wahala da kuma samun nishadi, motsa jiki da cin abu marar nauyi.

2. Lura da abubuwan da ake ci lokacin al’ada ko karatowarta, da rage cin gishiri don yana tara ruwa ya kuma hana shi fita idan ya yi yawa sai jiki ya fara nauyi da kumburi. A kuma guji cin soyayyun abubuwa da gyada, yaji, kayan filawa, naskofi, lemon kwalba, goro, koko, barasa (giya). Don suna rikita lokacin al’ada. A rika yawaita cin ‘ya’yan itatuwa, shayi mai kyau don suna rage ciwo na mara.

3. A rage shan magunguna barkatai.

4. Za a iya amafani da magugunan karin jini idan haila ta yawaita. 5. Idan mara ko ciki na ciwo sosai, za a iya kwantawa waje daya ta hanyar jingino da matashi da kuma yin numfashi kamar ana haki.

6. Akan kuma iya bada nauyi ta kasa da doka gadon baya ko shafa kan mara idan har ta kulle da ciwo. Haka kuma idan ciwon ya yi tsanani da yawa, akan iya jika tawul da ruwan zafi ko sanyi a dora a saman mara ko goshi, hakan kan kawo sassaucin ciwon. A lura da tsafta da kayan amfani na yau da kullum kamar abinci, sabulu, man shafawa. Abubuwa da dama kan faru, amma mafi kyautatuwa shi ne zuwa asibiti.

Yawancin mata suna fama da canjin yanayin jiki, ciwon mara, yawan bacci ko rashin bacci, fushi marar dalili, ko jinin haila yana zuwa matsala, kuma galibi hormonal imbalance ne ke haddasa hakan, Amma sai taita treating wani abin kuma in hormones din nan ba suyi dai dai ba ba za ki ji dai dai ba.

 

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Za A Magance Amosanin Baki
Ado Da Kwalliya

Yadda Za A Magance Amosanin Baki

October 4, 2025
Hadin Tsumin Baure
Ado Da Kwalliya

Hadin Tsumin Baure

September 27, 2025
Gyaran fuska
Ado Da Kwalliya

Gyaran Fuska Da Laushin Fata

August 30, 2025
Next Post
Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

Babban Sakataren SCO: Sin Na Taka Rawar Gani A Matsayin Kasar Da Ke Shugabancin SCO

LABARAI MASU NASABA

gaza

Majalisar Dattawa Ta Maido Da Ranar Tantance Sabbin Shugabannin Sojoji Zuwa Laraba

October 28, 2025
Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

Duk Da Barazanar Tattalin Arzikin Duniya, Kasar Sin Ta Sanya Tabbaci Da Kwanciyar Hankali A Duniyarmu Mai Cike Da Ruɗani

October 28, 2025
Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

Ina Fatan Buga Kofin Duniya Na 2026 — Messi

October 28, 2025
Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

Tsohon Kwamishina Ya Zargi Gwamnatin Kano Da Sayar Da Filin Makaranta Kan Miliyan 100

October 28, 2025
An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

An Matsa Min Sai Na Koma Jam’iyyar APC – Gwamnan Filato

October 28, 2025
’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

’Yansanda Sun Ƙaryata Rahoton Ƙone Gidan Shugaban Jam’iyyar PDP A Bauchi

October 28, 2025
Mutum 18 Sun Mutu, 40 Sun Jikkata A Hatsarin Mota A Kebbi 

An Kashe Mutum 10 A Harin Ramuwar Gayya A Jihar Kebbi

October 28, 2025
Ganduje Na Kara Shan Matsin Lamba A Kan Ya Sauka

Zargin Almundahana: An Ɗage Shari’ar  Ganduje Da Matarsa Saboda Rashin Miƙa Takardu

October 28, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

Sojoji Sun Kashe Masu Yi Wa ISWAP 4 Safarar Makamai A Borno

October 28, 2025
Ciwon

APC Ta Yi Barazanar Dakatar Duk Kwamishinan Da Bai Sanya Irin Hular Tinubu Ba

October 27, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.