• English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Matsalar Bindiga Tana Addabar Amurka Matuka

by CMG Hausa
3 years ago
Bindiga

Yau watanni 3 da suka wuce, wani dan bindiga ya kashe kananan yara 19 da malamai 2 a makarantar firamare ta Robb a kasar Amurka.

A lokacin, shugaba Joe Biden na kasar ya lashi takobin daukar hakikanin matakai, tare da sa hannu kan shirin dokar kayyade sayen bindiga a watan Yuni, wanda a cewarsa, shirin doka ne mafi muhimmanci cikin shekaru 30 da suka wuce kan harkokin bindiga. Amma fararen hula da ba su ji ba su gani ba suna mutuwa sakamakon harbe-harben bindiga.

  • IAEA: Za A Tattauna Batun Hadin Gwiwa Tsakanin Amurka Da Birtaniya Da Australiya

A karshen makon jiya, an yi harbe-harbe a wasu jihohin Amurka. Me ya sa Amurka, wadda ke matsayin kasa mafi arziki a duniya, ba ta sa aya ga laifuffuka masu nasaba da bindiga ba?

Masharhanta sun yi nuni da cewa, dalilan da suka sa hakan su ne: tanade-tanaden dake cikin gyararren shirin doka na 2 na kundin tsarin mulkin kasar dangane da mallakar bindiga, da kuma sabanin dake tsakanin jam’iyyun siyasa 2 na Amurka kan sa ido kan harkokin bindiga.

Har ila yau, matsalar bindiga tana yin kamari sakamakon yawan riba. Girman kasuwar kera bindiga da cinikin bindiga ya kai dalar Amurka biliyan 70.5 a kasar a shekarar 2021.

LABARAI MASU NASABA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Kungiyar kula da harkokin bindiga ta Amurka NRA wadda ke matsayin rukunin tattalin arziki mafi tasiri a kasar, tana ba da taimakon kudi ta fuskar siyasa a kowace shekara, tare da zuba makudan kudade kan yayata muhimmancin mallakar bindiga bisa doka, a kokarin kawo tsaiko ga yadda gwamnatin take daukar matakai masu nasaba da bindiga.

Kamar yadda jaridar The New York Times ta bayyana, kusan kowa da kowa na rayuwa cikin tsoro a kasar Amurka sakamakon karuwar harbe-harben bindiga a kasar.

Me ya sa haka? Domin masu kudi suna jin dadin ganin karuwar dukiyoyinsu sakamakon kera bindiga da cinikinsa, kana ’yan siyasan Amurka suna ta samun taimakon kudi ta fuskar siyasa ba tare da tsayawa ba.

Har zuwa yanzu ba a san yaushe Amurka za ta fitar da kanta daga yanayin tsoro sakamakon matsalar bindiga ba. (Tasallah Yuan)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko
Daga Birnin Sin

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana
Daga Birnin Sin

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Next Post
’Yan Sama Jannati Na Kasar Sin Sun Gayyaci Matasan Duniya Da Su Ziyarci Tashar Sararin Samaniyar Sin

’Yan Sama Jannati Na Kasar Sin Sun Gayyaci Matasan Duniya Da Su Ziyarci Tashar Sararin Samaniyar Sin

LABARAI MASU NASABA

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

Kotu Ta Ba Da Umarnin Kama Tsohon Shugaban INEC, Mahmood Yakubu, Kan Saɓa Umarninta

October 9, 2025
Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

Gobara Ta Sake Ƙone Kasuwar Oba A Benin

October 9, 2025
Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

Kofin Duniya U-20: Argentina Ta Lallasa Nijeriya Da Ci 4-0

October 9, 2025
Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.