Wakilinmu da ke Zariya a Jihar Kaduna ISA ABDULLAHI GIDAN BAKKO, ya sami damar tattaunawa da wata matashiyar maruciya mai suna HAJIYA HAFSAT MUHAMMAD BARA’U, wadda ‘yar asalin karamar hukumar Sabon Gari ce a Jihar Kaduna da ta rungumi rubuce–rubuce, domin wasu dalilai da ta bayyana a hirar da suka yi, ga dai yadda hirrar ta kasance.
Da farko, ko za ki bayyana mana cikakken tarihin ki?
Tarihi na ba wani mai tsawo ba ne, amma zan bayyana maku cikakken tarihi na. Kamar yadda ya shaida maka, suna na, an haife ni ne Sabon Garin Zariya da ke jihar Kaduna a shekara ta 1987, bayan iyaye na sun sa ni a makarantar Allo a zuwa na Islamiyya, kamar yadda ka sa ni na kyakkyawar al’adar nan ta al’ummar Arewacin Nijeriya, ni ma na amfana da wadannan makarantu da na ambata na Allo da kuma Islamiyya. Iyaye na sun sa ni a makaranatar firamare ta ‘ya’yan da ake kira da sunan ‘ DEPOT L.E.A ‘’ bayan na kammala wannan makaranta, sai na sami shiga sakandaren Hassan Gwarzo da ke Kano, ina kammalawa sai na sami shiga kwalejin kimiyya da fasaha da ke Sakkwato, bayan na dawo gida Zariya sai na sami shiga wata makaranta da ake kira a sunan ‘ELITE‘’ da ke Zariya inda na karanta wani bangare na kiwon lafiyar al’umma, yanzu haka, na kammala duk shirye–shiryen da suka kamata, domin ci gaba da karatu a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya.
Har tun takacin lokacin da ki ka bayyana mana karatun da ki ka yi, ya na nuna zuwa yau, ba ki taba yin aikin gwamnati ba ke nan ?
Lallai ban taba yin aikin gwamnati ba ko kuma na kamfani, amma a rayuwa ta babban abin da ke cikin zuciya ta shi ne in ga na dogara da kai na ta sana’o’in hannu da na ke yi a gidanmu tun ma kafin in yi aure.
Cikin sana’o’in da na runguma sun hada da hada turaren wuta da kananan magunguna na cututtukan da suke addabar al’umma da, babu ko shakka da wannan sana’a na dogara domin samun abin da zan biya wa kai na bukata da na sauran al’ummomi da uke kusa da kuma nesa da ni.
Yau ga shi kin rungumi harkar rubuce–rubuce, me ya baki sha’awar rungumar wannan babban aiki na rubuce–rubuce.?
Babban dalilin da ya san a rungumi rubuce–rubucen litattafai shi ne, domin yadda na lura da matsalolin da suke faruwa a tsakanin ma’aurata, wadannan matsaloli dana lura da su, su suka sana fara tunanin bayar da gudunmuwa ta ga mata ‘yan uwa na, ta yadda za su sami mafita daga wadannan matsaloli da a wasu lokuta ke haifar da rabuwar aure a tsakanin ma’aurata da mu ke tare da su.
Sauran matsalolin da suka dade su na damu na sun hada da mu’amalar da ke tsakanin ma’aurata, na dade da lura ba a zaman takewar addini ba a kuma yin na al’ada, ga kuma matsalolin zamantakewar iyayen mata da matan ‘ya’yansu, duk wadannan matsaloli na yanke shawarar in bayar da gudunmuwa a rubuce ta yadda ‘yan uwa na mata za su karanta matsalolin, su kuma karanta mafitan matsallin da na bayar a rubutun littafi na farko da na rubuta mai suna ‘’ HASKE A KAN MA’AURATA, TSABTA DA TARBIYYA’’
A dai wannan littafi, na yi tsokaci mai tsawo kan tarbiyyar yara a tsakanin iyayensu, wato uwa da kuma uba, dukkanin matsalolin na fito da maiya yawansu, na kuma bayar da shawarwarin yadda za a fita daga matsalolin a cikin sauki, ba tare da an sami wani dogon lokaci ba.
Babu shakka, batun aure, wasu mazan sun dauki aure da sauki, tamkar gasa a tsakanin maza, su kan dauka, in aboki na ya na da mata biyu ko uku ko kuma hudu, wadannan su na cikin dalilan rubuta wannan littafi da na ambata.
Abin nufi, mazan bas u da dalilin tara matan, su kuma matan bas u san hakkokinsu da ke kan mazansu ba, dukkanin wadannan matsaloli, na bayyana su a wannan littafi, sai dai tsakure na yi tare da misalai da wanda ya karanta littafin zai fahimta a cikin sauki.
A kwai wani ko kuma wata marubuciya da ki ka yi koyi da salon rubutunsa ko kuma rubutun ki ?
Babu shakka ko da rana guda ban yi tunanin wanke fasahar wani marubuci ko kuma wata marubuciya ba, abin da na yi kawai shi ne, na yi amfani da ilimin addinin musulunci da na ke da shi wajen sa tunani na a takarda har zuwa yau da ya zama littafi, tun ina karama na fara tunanin zama marbuciyar da za ta isar da sakon gyara ga al’umma maza da kuma mata, a yau, zan iya cewar, bukata ta biya, tun da Allah ya cika ma ni burin a, na fitar da littafin farko, kamar yadda na bayyana a baya.
Yaushe ki ka fara tunanin dora alkalami a kan takarda, domin rubuta littafi ?
To wannan tambaya ta na tsauri, domin farar da garaje, b azan iya cewar ga shekarar da na fara rubutun wannan littafi ba, amma, zan iya cewar, a kalla yau na shafe shekara goma sha bakwai ina yin wannan rubutu a hankali dare da kuma rana, har zuwa lokacin da na kammala watannin kadan da suka gabata, abin da iya tunawa dais hi ne, duk lokacin da wani abu da zama tobali wajen gina wannan littafi, ko da ina kicin ne, a matsayi na na matar aure, na kan nemo takarda a cikin gaggawa in rubuta abin da ya zo ma ni, daga nan ne na tattara wadannan takardu bisa tsari suka zama littafin da na ambata.
Sakon da ki ka aika wa al’umma, wanne salon rubutu ki ka yi,salon wake ko kuma rubutun zube ?
Ai ta rubutn zobe nay i, ba wake ba, kuma a salon rubutun, nay i amfani da kalmomin da duk wanda ya karanta littafin, ba zai fuskanci matsalar rashin fahimtar sakkon ba da kuma misalan da na bayar a rubutu na, komi a cikin sauki ne.
Ya batun neman shawara daga fara rubuta littafin zuwa wannan lokaci da ki ka kammala ?
A gaskiya, ban taba zuwa wajen wani ko wata domin neman shawarar rubutun wannan littafi ba, sai dai mai gida na, da ya ba ni duk goyon bayan da ya kamata, bai taba fushi da ni ba, in ya fahimci na dukufa wajen yin rubutun wannan littafi da kuma wasu ‘yan uwa na da lokaci ba zai ba ni damar bayyana sunayensu ba.
Wasu matsaloli ki ka fuskanta a lokacin da ki ka motsa wajen mayar da rubutun ki littafi ?
Lallai na fuskanci matsaloli, musamman, wasu takardun sun bace a lokacin da na fara tunanin mayar da rubutu na littafi, amma da ya ke da taimakon mai gida na da wasu kawunni na, matsalolin sai suka zama tarihi tare da zama darasi, da na fahimci, duk wata takarda da na rubuta, na sami wajen ajiya guda daya, da na motsa na san inda zan ga takardun.
Sauran matsalolin sun hada da yadda na kula da hidimomin gida a matsayi na matar aure da kuma kula da yara, dukkanin wadannan abubuwa da na bayyana, ba su zama ma ni gagabadau ba da zai sa in dakata wajen rubuta wannan littafi.
Mu na godiya da wannan dama da kika bamu, mu ka yi wannan tattaunawar da ke.
Ni ke da godiya, Allah ya ci gaba da yin jagoranci ga wannan jarida da kuma daukacin ma’aikatanta, amin.