Kamar kowanne mako wannan shafi ya kan zakulo muku batutuwa daban-daban da suka shafi al’umma, kama daga fannin zamantakewa na rayuwar yau da kullum, rayuwar zaman aure, rayuwar matasa (soyayya), Siyasa, da dai sauransu.
Inda a yau shafin zai yi tsokaci ne game da abin da ya shafi Fyade ga ‘ya’ya Mata. Duba da yadda wasu iyayen ke fuskantar irin wannan kalubalen ga yaransu da su kansu Yaran. Fyade dai wani babban al’amari ne wanda mata ke riskar kansu ciki, ta yadda namiji ke kokarin ganin ya kawar da budurcin ‘ya mace ba tare da amincewar ta ba.
Ko me ya ke kawo yawan Fyade ga ‘ya’ya mata? Shin laifin waye? Ta wacce hanya za a magance matsalar? Dalilin hakan ya sa wannan shafi ya ji ta bakin wasu daga cikin matasa game da wannan matsalar, in da suka bayyana ra’ayoyinsu kamar haka:
Fatima Sunusi Rabiu Marubuciya daga Jihar Kaduna:
Abin da ke kawo yawan fyade ga ‘ya’ya mata da farko akwai son zuciya na wasu daga cikin maza. Wani za ka ga rumi-rumi yana soyayya da yarinya, da ta yarda da shi sai ka ga ya rusa mata rayuwa, duk da wani lokacin akwai sakaci na wasu matan, saboda yawan shigar mazan da suke yi yana jawo hankulan wasu mazan har su kai ga yi musu fyade.
Wasu kuma neman duniya ne, yayin da wasu kuma son zuciya ne, sai ka ga dattijo mai yawan shekaru yayi wa karamar yarinya fyade saboda neman duniya ko son rai, Allah ya kyauta ya shirya mana zuri’ar musulmi baki daya, Amin.
Maganar gaskiya wani lokacin laifin matan ne, saboda irin shigar da suke ta daukar hankali. Wani lokacin kuma laifin mazan ne domin akwai masu matacciyar zuciya mara kyau da rashin tsoran Allah, sai ka ga wani lokacin ma dan uwa ne na jini, ko makwabci, ko wani da wata dangantaka ta hada, saboda rashin imani da son zuciya suke aikatawa ‘yan uwarsu wannan mummunan abu.
Da farko dai iyaye su sanya ido ga ‘ya’yansu ta hanyar hanasu shigar da ba ta dace ba, sannan hukunci wato gwamnati ta ba da gudummawa ta hanyar rataye duk wanda ya aikata fyade, idan har kai tsaye ana kashe duk wanda ya aikata! Tabbas masu niyyar yi suma za su fasa.
Iyaye su saka ido akan yaransu da basu tarbiyya ta gari. ‘Yan mata kuma a guji shigar banza da amsa gayyatar saurayi, ko zo ki rakani gidan Yayata da sauran ire-iren hakan. Mutane kuma su zamo masu tsoran Allah abin da ba za ka so ai wa ‘yar cikinka ko wata a ahlinka ba kar ka yi wa ‘yar wani ko ahlin wani. Ina addu’ar Allah ya sa a zartar da hukuncin kisa ga duk wasu masu aikata fyade. Ummu Affan marubuciya.
Fadila Lamido daga Jihar Kaduna:
Toh! a tunani na abin da ke kawo yawan fade ga ‘ya’ya mata a yanzu ba zai wuce rashin hukunta masu laifin da ba a yi ba, yawanci idan an kama me laifi ba za a nuna wa duniya irin girman hukuncin da aka yanke masa ba, wanda zai zama izina ga ‘yan baya, sai dai a kama me laifin kwana kadan kuma a sake shi, haka za ka gansu suna yawo cike da gadara, yayin da wasu kan canza gurin zama saboda kunya ko kuma saboda tsoron ‘yan unguwa, kuma ko da sun bar unguwar ba shi zai hana su kara aikata irin laifin ba, saboda sun san ba a yin hukuncin da ya dace.
A duk lokacin da irin wannan ya faru ba za mu kira shi da laifin iyaye kai tsaye ba, duk da cewa ta wani bangaren suna da laifi, wasu iyayin za ka samu suna ba da matukar tsaro da kulawa akan ‘ya’yansu, amman duk da haka sai irin hakan ta faru akan yaran, idan ba ka saki yaron a titi ba na gida ma sai ya aikata abun da ba kai tunani ba. Wasu a makaranta, wasu ma a hanyar makaranta, wasu iyayen kuma da kansu suke jawo wa kansu matsalar, dalilin dora wa yara mata tallan da suke yi, irin wannan iyayen na kan ga kamar sun sallama yaran ne, duk ma halin da za su shiga kawai su kawo musu kudi, domin duk wadda ya sake yarinya mace ta fita talla a tunani na ya fi bawa kudin mahimmanci akan rayuwar yariyar shi.
Yara mata kanana sai ka gansu a cikin kasuwanni wai suna talla, kina uwa har yaushe za ki samu nutsuwa bayan ‘yar ki tana cikin tsakiyar kasuwa, ai gomma ace ki tura ‘yar makaranta ke uwa ki dauki talla tunda ke kina gane fari kina kuma gane baki, kana zaune da yaran a cikin gida ma fa ba ka da wani kwanciyar hankali, Ko da yaushe uwa so take ta ji danta kusa da ita, ko wasa suke a cikin gida cikin kwala kira kake, domin ka san suna nan inda kake so ko kuma sun dan matsa, kuma ba dan kana zargin wani ba sai dan rashin nutsuwa, domin yadda abubuwan ke faruwa akwai daga hankali. Na cikin gidan ma ba ka da tabbacin ba zai aikata ba, bare wadda za a hadu da su waje, dan haka rashin kishin ‘ya mace ne tura ta talla, kuma ya dace ace idan aka samu ‘yar da aka tura talla an mata fade a hade me laifin da iyayen a hukunta su baki daya, dan suma masu laifi ne.
Amma sai ka ga suna kuka suna cewa a taimaka musu a kwatar wa ‘yar su hakkinta, alhalin su ne suka tura ta, wadda suka bawa yaran kulawa daga gida sai makaranta idan irin haka ta afku akan yaran su ne ya kamata su yi kuka ba wadanda suka tura yaran talla ba. Idan ko har kika tura ‘yar ki talla to kisa a zuciyar ki komai na iya faruwa. Shawarata ga iyaye su kara saka Ido sosai akan yara, masu dora wa yara mata talla, kuma su kuka da kansu su bari. Su kuma hukumomi su ji tsoron Allah su dinga hukunta me laifin yadda dokar kasa ta tanadar, Allah ya sa mu dace.
Hafsa Umar Nasir Jihar Kano Karamar hukumar Gaya:
Rashin ilimi da yawan dorawa yara talla, sannan iyaye su ce dole sai sun kawo kudi gida dukka, ko su hanasu abinci wannan ya sa yara suke bi kowacce hanya wajen samo kudin. Laifin iyaye ne saboda ba sa lura da yaransu musamman uwa mace saboda ita ke zaune da ‘ya’yanta ta san halin kowa.
Ta hanyar daukar mataki ga wanda ya aikata wa ‘ya’yansu fyade wajan hukuncin dole ya auri yarinyar, kuma ya rike yaron da aka haifa. Ina bawa iyaye shawara su bawa yarnsu ilimi, sannan su nuna musu illar hakan, sannan uwa mace ta rinka lura da lokacin da yarinyar ta take al’ada saboda hakan zai ba da gudumuwa ta gane wanne hali yarinyar take ciki da kuma lura da guraren.
Su kuma ‘yan uwana mata ina basu shawara akan ka da abin duniya ya rudesu har su bayar da rayuwarsu akan kudi, idan mutum zai siya abin tallanki ya baki kudinki a gaban mutane, ka da ya ce ki zo gida ko shago ko kango ki karba, ki bishi zai cutar da rayuwarki. Wannan shi ne a takaice Allah ya sa mu dace.
Ibrahim Danmulky, Jihar Kano karamar hukumar Nassarawa unguwar Gama:
A gaskiya ni a ra’ayina abin da yake kawo yawan fyade a zamanin nan yana da yawa, amma daga cikinsu wadanda suka fi karfi su ne;
Rashin kulawa da rayuwa matasa da kuma tsofaffi na gida. Tallace-tallacen da ya’ya mata suke yi. Shigar nuna tsiraici da matan zamani suke yi yanzu. Laifin yawanci na iyaye ne da su kansu matan. Hanyar da za a bi a magance matsalar nan ita ce; addu’a da kuma taimakon gwamnati wajen tallafawa masu rauni. Shawarata ga iyaye su ji tsoron Allah, su daina tura ‘ya’yansu mata tallah, kuma kananun yara a dinga suturce su, Sannan kuma Al’ummar gari mu ci gaba da addu’a.
Abba Abubakar Yakubu, (Shugaban kungiyar Jos Writers Club):
Matsalar Yawaitar Fyade Matsalar Tarbiya Ce; Muhawarar wannan mako tana da muhimmanci sosai, kasancewar yadda matsalar fyade ke kara yawaita a cikin al’ummar mu. Fyade tsohuwar matsala ce da ta dade tana zama kalubale a tsakanin al’ummar duniya, domin kuwa babu wata al’umma da ba ta fuskantar wannan matsala. Ko da yake ya danganta ga inda ta yi tasiri, da inda ta yi karancin, saboda yadda tarbiyya da doka ke aiki.
Fyade dai yana nufin saduwa da mace ta hanyar jima’i ba da amincewar ta ba, ko ta hanyar karfi, tsoratarwa, ko ta hanyar bugarwa da sanya wani magani ko abin maye da zai gusar da hankalin mutum, ko ya sa barci da kasala mai nauyi, ko kuma ta hanyar yaudara.
Masana da masu kare hakkokin dan Adam na ganin duk wata siga ta jima’i da za a yi da mace ko namiji, babba ko karamar yarinya da karamin yaro, ba da yardar su ko hadin kansu ba, duk yana matsayin fyade ne. Har ma da masu ganin ko da matar mutum ce, in ba da amincewar ta ba ne, shi ma fyade ne. A muhawarar da muke yi, ana so ne a mayar da hankali kan fyade da ake yi wa ‘ya’ya mata, musamman kananan yara.
Wannan shi ne ya fi yawaita a halin yanzu, kuma hakan na faruwa ne a dalilin rashin tarbiyya da za a iya cewa shi ne yake jawo wa. Yara maza yawanci tun suna kanana a wasu wurare suna wasannin banza ko wasannin miji da mata, kuma ba a ganin hakan a matsayin wani abu, har ma a kai ga yaro namiji mai wayo ya rika yi wa kananan yara mata wasa da al’aurar su, ba a dauki mataki ba.
Har zuwa inda zai fara gwada amfani da kananansa yayin da shekarun sa suka fara haura bakwai zuwa goma, lokacin da wasu a cikin gidaje ke kallon abin da kuruciya, har suna cewa “ai ya yi Washin Aska ne”, musamman bayan wani lokaci da warkewar kaciyarsa.
Matsalar iyaye masu karancin tarbiyya ko wadanda aka yi wa auren wuri, ba su samu kyakkyawar tarbiyyar da ta dace ba, har suka fara samun yara, kuma sun tashi a cikin yanayin da tarbiyya ke kara tabarbarewa.
Cudanyar wasu yara maza da manyan yayu da suka balaga shi ma yana kara bude tunanin yaro ya taso da sha’awar yin abin da yake ji ana labari ko abin da yake gani na batsa a wayoyinsu.
Haka ma a bangaren ‘ya’ya mata gwamutsa kananan yara mata da manya yana gurbatawa kananan tunaninsu har ya fara kusantar da su wajen maza. Aiken yara kanana cikin maza a wuraren da ba na jama’a ba, shi ma yana sa su cikin tarkon wasu gurbatattun maza.
Yawaitar maza marasa aikin yi a cikin anguwa, yana sa kananan yara da ‘yan mata cikin hadarin fuskantar fyade, saboda balagaggun maza da ke zaune cikin anguwa babu damar yin aure ko samun mace a kusa da su, za su iya kai musu farmaki.
Tallace tallace da ake dorawa yara mata yana sa su shiga cikin manyan maza marasa tarbiyya da kamun kai, kuma su ma suna iya amfani da wannan damar su hurewa yaran kunne, har su aikata musu abin da ba su shirya saninsa ba. Yawaitar magungunan kara sha’awa na maza da mata a tsakanin al’umma, babu sakayawa babu doka, shi ma yana jefa rayuwar yara cikin hadarin fyade. Domin duk namijin da ya sha magani bai samu yadda yake so ba to, idanunsa rufewa suke yi ya afkawa duk macen da ya samu kusa da shi.
Yawaitar shaye-shayen kwayoyi da sinadarai masu bugarwa na sa duk wanda yake cikin maye ba tare da sanin ina hankalinsa yake ba, ko kasa bambance daidai da ba daidai ba, shi ma yana iya sa shi ya afkawa duk macen da ya gani, komai kusancin sa da ita, ko da kuwa ýar cikinsa ce ko uwarsa mahaifiya. Rashin amfani da tsauraran dokoki daga bangaren gwamnati ko hukumomin tsaro, ko kuma sasantawa a tsakanin iyaye, yana sa fyade ya ci gaba.
Domin duk wanda ya saba, ba zai iya dainawa ba, sanin cewa, babu abin da zai same shi. Lallai ne iyaye su tsayu da al’amarin tarbiyyar ‘ya’yansu, a yi riko da koyarwar addini, a rika raba yara maza da mata, manya da kanana. Sannan a rika barin doka tana aikinta a kan duk wanda aka kama da hannu a laifin fyade. Hukumomi kuma su tsayu a kan aiki da dokokin da aka sanya na yaki da fyade, don ya zama abin misali ga masu kunnen kashi. Jama’ar anguwanni a rika sa ido ana tsawatarwa.
Hamidan Badamasi Rijiyar Lemo Jihar Kano:
Rashin kula da yara da kuma aikasu waurin da bai kamata da alaka da mazan da ake da shakkar tarbiyyar su shi ne ummul-aba’isin dake haddasa fyade a wannan zamani da muke ciki, amma wani lokacin, a gefe guda bokaye ma na haddasa wannan lamari wajen umartar mutanen da suka je wajensu neman wata bukata.
Babu shakka laifin iyaye ne ta yafda za ka samu wasu iyayen kan koyawa yaransu son abin duniya tun suna kanana wanda wannan dama ce marassa imanin kan yi amfani da ita wajen farauto zuciyar yaran. Hanyar da za a magance matsalar fyade shi ne; Dole sai iyaye sun sanya ido akan shige da ficen ‘ya’yansu da kuma sanin wa suke alaka da su a waje, kuma su rage nuna musu son abin hannun mutane da hanasu shiga ko aikensu inda bai kamata ba musamman wajen mutanen da ake tan-tamar tarbiyar su, Shawarata ga iyaye mata; Su ji tsoran Allah, su sani cewa dukkan wadannan yara da Allah ya basu amana ce akansu kuma tabbas sai Allah ya tambaye su ranar kiyama kan wannan amana, ina kara kira ga iyaye su zama masu sanya ido da shige da ficen ‘ya’yansu, da sanin mutanen da suke mu’amala da su idan sun fita, domin sakin yara da kuma rashin sanin wadanda suke mu’amalar da su kan jefa su cikin mawuyacin hali.
Aminu S. Garba Halliru Tukuntawa Digar Gidan Maza:
Abin da yake kawo fade ga ‘ya’ya mata mafi yawanci kwadayi ne da san abun duniya da yayi yawa, wani lokacin daga iyaye, wani lokacin daga Matan wajen kallon kawaye, da sawa a rai ta hanyar cewa ita ma sai ta yi abun da kawar ta yi ko ta halin kaka. Gaskiya kaso 100 daga bangaran iyaye ne saboda rashin sa ido a ma’amular ‘ya’yansu.
Hanyar da za a magance wannan matsalar shi ne; Dole ne ‘iyaye su sa ido sosai ga ‘ya’yansu game da tarbiyar kawayan da suke mu’amala da su da lura a duk inda suke zuwa. Shawara daya ce iyaye su ji tsoron Allah su kula da hakkin da Allah ya dora musu iya karfinsu su daina fifita san duniya akan tarbiyyar ‘ya’yensu.
Muhammad Kabir Kamji (M.K) daga Jihar Katsina:
Abin da ke jawo ko wane lokaci ake yi wa kananun yara fyade dalilan suna da yawa, daga cikin su akwai; kauce hanya, ma’ana idan kana neman wani abu na duniya, hakan zai sa bokan da kaje gurinsa ya sanar da kai sai ka yi fyade, sannan akwai shigar da idan mace tayi shi ma zai iya zama hanyar da za a yi mata fyade.
Maza suna da nasu laifin haka mata ma suna da nasu laifin. Da zarar namiji ya fara jin sha’awa ayi masa aure, sannan ita ma macen ayi mata aure, kuma a hanata sanya kayan da ba su dace ba. To alhamdullahi ala kulli halin, shi dai fyade fasadi ne a cikin al’umma, sannana al’umma sunan dacewa duk abin da kayi za a yi wa naka. Sannan su ma matan suna taka rawar gani wajen aikata fasadi.
Abdulrrashid Haruna Kano:
Babu shakka babban dalilin da ya fiya kawo lalata irin ta fyade a cikin al’umma shi ne; Yaro ya taso Mace/Namiji ba da samun kyakkyawar kulawa ba, ya taso har zuwa zaman sa baligi yana yi wa fyade kallan abu wanda yake ba wani abu na azo a gani ba, a lokacin da ya fara wannan nazarin zai fara sha’awar aikata shi, domin cikar burinsa, Allah ya kare ya kuma kiyaye. Laifi a bayyane yake, laifin iyaye ne domin kulawa tana gyara komai, haka rashin kulawa tana bata komai, akan idan mu muna iya tan-tance yaran da duk suke aikata wannan ba dala cewa ba su samu kyakkyawar kulawa ba, wasu kuma yana iya faruwa su tasa a gida da ba’a nuni da cewa hakan ba dai-dai bane, kuskure ne. Ko kuma ma wasu ya zamo tsanani na rayuwa har ya kai ga subhanallah Allah ya kare mu baki daya.
Hanyoyin suna da yawa amman kadan daga ciki sune yaro/yarinya ta tasa a gida da samun kyakkyawar kulawa da hani da duk abin da zai iya sa yaro tunaninsa ya bi wannan hanya, sanar da shi illar aikata fyade tun kafin ya san yadda ake yi/kuma da wa ake, a sanar da shi addini sannan a bashi ilimi na addini dana zamani, a nuna masa ya kare kansa da dukkan abin da zai yi na ba dai-dai ba, ba iya wanda zai iya kai shi ga afkawa ga wannan hali ba da wasu ma da dama.
Shawarata ga iyayenmu shi ne; su kara zage dantse gun yunkurin sauke hakkin da Allah ya ba su akan yayan su, su kara sani cewa duk dan da aka haifa lafiya kalau ake haifar sa, bai san yayi shaye-shaye ba ko sata bare kuma fyade, saboda haka mu sani randa muka koma ga Allah, Allah zai tambaye mu akan amana ta ‘ya’ya da ya bamu, ya akai mu kai sakaci haka ya faru? saboda haka iyaye mu kara kulawa.
Mansur Usman Sufi (Sarkin Marubutan Yaki) Jihar Kano Nijeriya:
Gaskiyar magana abin da ya kawo yawan fyade ga ‘ya’ya mata abubuwa da yawa, amma manyan su ne; Sabawa al’ada da addininmu. musamman bayyana tsiraici ga ‘ya’ya mata ta hanyar yin dinkin da bai kamata ba.
Wadanda dole ne su ja hankalin Mazaje har su yi tunanin hakan. Na biyu shi ne; yada labaran fyade da ‘yan jarida ke yi da sauran al’umma. Kuma dukkan al’umma suna da laifi domin da na kowa ne, amma iyaye sun yi kaso mafi tsoka wajen aikata laifin. Hanyoyin da za a magance su ne; Suturce tsiraici, da nisanta yara da wadanda suka balaga ko da muharramansu, kuma a daina yada labarin cewa; wani ya yi fyade. Tunda gashi kullum ‘yan jarida rahoto suke yi amma kullum fyade karuwa yake, to bayyana sabon Allah shi ma yada shi ne. Shawara ga iyaye shi ne; su koma tsarin al’adar Hausawa mai kyau da kuma tsarin addinin musulunci.
Musbahu Muhammad daga Jihar Kano Unguwar Goron Dutse:
Jahilci, Neman Duniya, Barin ‘ya’ya mata a sake babu kwaba da kuma shigar banza. Laifin Iyayene, dangin iyaye da kuma al’ummar da ake rayuwa tare da Su. Iyaye su kasance tare da ‘ya’yansu, su ja su a jiki, su yi hira da su, sannan su dinga kulawa da shige da ficensu, Mu’amalarsu da kawayensu. Iyaye ya kamata su sani ‘ya’yansu amanar Allah ne a gurinsu, dan haka su kula da su yadda addini ya tanadar. ‘Ya’ya mata su sani duk abin da suka aikata mara kyau hakan zai cutar da rayuwarsu ta duniya da lahira. Su kuma al’umma su sani cewa saka Ido dan kulawa da tarbiyyar ‘ya’ya aiki ne na kowa da kowa ya kamata a kula ayi aiki kyakkyawa don samun kyakkyawar zuri’a.
Gaskiya akwai rashin tsoron Allah mutanan da suke yin fyade. Eh! to laifin masu yi ne mana, ai ba za ka dora wa wanda aka yi ma abu ta karfin tsiya laifi ba. Iyaye su kula da rayuwar ‘ya’yansu sosai wajen dukkan wani motsin ‘ya’yansu. Yin hukunci mai tsanani sannan kuma ayi shi a bayyane saboda wasu su gani.
Abba Fagge Karamar hukumar Fagge Jihar Kano:
Abin da yake kawo fyade dalilai ne masu yawa misali; Shi mai yin fyaden da kuma wacce ake yi wa fyade wajen namiji son zuciya da kuma rashin tausayi da kuma son duniya, wasu kudi ke sa su wasu son zuciya, wasu kuma misali wadda yayi wa yarinya ‘yar shekara uku fyade wannan son zuciya su kuma mata a bangaransu akwai wacce laifinta ne saboda shigar banza da nunawa namiji abin da bai dace ba, a takaice kenan. Laifin kowanne mata/maza iyaye ‘yan uwa abokai dukansu suna da laifi. Hanyar magance wa shi ne; daina shigar banza, daina sakin yara sakaka, yi wa maza aure rage wahalar aure shi ne hanya. Shawarata iyaye su kara kulawa da ‘ya’yansu yaransu da manyansu, su kuma maza su yi hakuri su ji tsoron Allah, sannan suna yin aure da kuma addu’a.