Bacin rai da alhinin rashin wutar lantarki, ya mamaye dukkanin fadin lungu da sakunan Najeriya. A yayin da bangaren samar da wutar lantarki kuma, ya cika da cin hanci, zalunci da kuma cin amana, wanda ko shakka babu; hakan ya bayyana ga ‘yan Nijeriya su kimanin miliyan 200 da doriya.
Abin haushi da takaici, kasa mai albarka kamar Nijeriya; amma kiri-kiri ana ji ana gani ta zama abin tausayi, sannan kuma ta zama tamkar wani fili; inda kowa ke cin karensa babu babbaka. Kazalika, dukkanin wani fata da miliyoyin mutane ke da shi; musamman ta fuskar samun walwala da ci gaban rayuwa, ya ruguje sakamakon matsalar cin hanci da rashawa, rashin sanin makamar aiki, kwadayi, sakaci da kuma rashin kishin kasa.
- Amurka Na Fakewa Da Guzuma Domin Harbin Karsana
- Shari’ar Zargin Karkatar Da Dukiyar Al’umma: Ganduje Da Iyalansa Ba Su Halarci Kotu Ba
Al’amarin Nijeriya ya zama tamkar wata almara, domin kuwa masu rike da madafun iko babu abin da suka sani sai gallaza wa ‘yan’uwansu, sakamakon samun kansu da suka yi a karagar mulki ta hanyar yin magudin zabe da almundahana, yayin da kuma tsarin mulki ya damka musu amanar al’ummar kasan a hannunsu, suka kuma yi biris da amanar tare da kokarin kai kasar ga rugujewa.
Babban jigon wannan yanayi dai shi ne, batun da ake ta faman cece-kuce a kansa; wato batun harkar wutar lantarki, da yadda ake hada-hadar kudaden wuta da kuma satar kudaden da aka yi a baya, matakin da shugabanni marasa hangen nesa da butulci suka wanzar. Haka zalika, an yi wa ’yan Nijeriya alkawarin samun ingantacciyar wutar lantarki tare da shelar ingantawa da ci gaban da zai haifar da tattalin arziki da kuma wadata. Amma duk da haka, wannan alamari ya kasance abin al’ajabi mai kuma matukar radadi, yayin da katsewar wutar lantarki, rugujewar layukan wuta (grid) da haraji mai yawa, wanda dubban dalilai tare da uzurin da kamfanonin wutar lantarki da kuma gwamnati ke ci gaba da shelanta wa al’umma, ke ci gaba da addabar su.
Har ila yau, wannan al’amari bai tike a nan ba, domin kuwa cire tallafin man fetur da aka yi a baya-bayan nan; ya sake jefa tattalin arzikinmu cikin wani yanayi maras dadi, lamarin da ya sa ‘yan Nijeriya sama da miliyan 200 shiga cikin firgici tare da gazawa wajen neman biyan bukatunsu. Haka zalika, batun hauhawar farashin kayayyaki; ya yi matukar yawa, canjin Naira zuwa Dala shi ma ya yi kamari, sannan kuma ga tsadar rayuwa ita ma ta zama wani abu daban ga talakawan wannan kasa.
A gefe guda kuma, alkawuran da aka yi na bayar da agaji; sun gagara cikawa, domin kuwa ba tsara abubuwan da suka kamata a yi don jin dadi ba, don rage radadi tare da saukaka wahalhalun da ‘yan kasa ke ciki ba, tuni an karkatar da kayan agajin da kyautu a bai wa talakawa zuwa ga ‘yan baranda da sauran abokan siyasar wadannan masu rike da madafun iko.
Karin albashin da aka yi, hasashe bai sa an samu yanayi na kwanciyar hankali ga masu aiki a ofisoshin gwamnati ko marasa aikin yi ko kuma wadanda ke cikin wani mawuyacin hali a wani bangare daban ko ’yan fansho ko kuma tsofaffi da sauran masu rauni ba. Kazalika, duk tsawon wannan lokaci; wadanda ke kan madafun iko da na zartarwa ko majalisa ko bangaren shari’a, na cike da jin dadi tare da sauran kayan alatu, watakila ba su sani ba ko kuma sun manta da wahalar da ‘yan Nijeriya sha a daidai wannan lokaci da ake ciki.
Kafa Tubalin Wargaza Ma’aikatar Wutar Lantarki (NEPA)
A shekarar 1950 ne aka kafa hukumar kula da madatsun ruwa ta Nijeriya (NDA), da kuma hukumar samar da wutar lantarki ta kasa (ECN), domin samar da wutar lantarki da rarraba ta. NDA da ECN sun kasance a matsayin Hukumomin Kula da Wutar Lantarki ta Kasa (NEPA) cikin shekar 1972, dominn inganta harkokin samar da wuta.
Wadannan kayayyaki da kadarori na kasa sun dauki kasar kimanin shekaru 46, ana samar da su daga 1960 zuwa 2007, wadda a rana tsaka wasu marasa hankali kuma macuta suka wancakalar wa kansu da abokan tafiyarsu.
Hukumar kula da kamfanoni ta kasa (NCP), karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa, ita ce ke tafiyar da harkokin kasuwanci da sayar da kamfanonin gwamnati; a yayin da ofishin kula da harkokin sayar da kadarorin gwamnati (BPE), ke sakatariyarta. Kazalika, a karkashinta ne aka kaddamar da shirin kwance damarar kamfanin wutar ta NEPA, a watan Maris na shekar 2005; lokacin da aka sake fasalin bangaren wutar lantarkin. Sannan, an rattaba hannu a kan dokar (EPSR), a matsayin dokar samar da tsarin doka; don gwanjon sayar da kadarorin NEPA da kuma shafe sawun wanda ya kai ga kafa ‘Kamfanin PHCN’.
Bayanai daga adireshen yanar gizon TCN, ya nuna bullar kamfanoni 18 da suka hada da Kamfanonin Makamashi guda 6 (GENCOs); ‘Egbin Electricity-1,320 MW’, ‘Kainji Hydro (Kainji -760 MW & Jebba -578 MW),’ ‘Shiroro Hydro -600 MW,’ ‘Delta /Ughelli Power-972MW,’ ‘Afam Power -650 MW, Geregu Power- 435 MW;’ kamfanin kula da harkokin wuta na Nijeriya, TCN da kamfanonin rarraba wutan lantarki guda 11, wato (DISCOs); Abuja DISCO, Benin DISCO, Eko DISCO, Enugu DISCO, Ibadan DISCO, Ikeja DISCO, Jos DISCO, Kaduna DISCO, Kano DISCO, Port Harcourt DISCO da kuma Yola DISCO.
Hukumar da aka bai wa alhakin sayar da hannun jari (BPE), dabarar da ta yi na kama da hanyar jari-hujja da satar dukiyar kasa da kuma kadarorin kasa. Wannan al’amari ya kasance a lokacin mulkin farrar hula na rashin kan gado da jam’iyyar barkakkiyar jar lema da wasu launukan ta yi.
An shaida wa ’yan Nijeriya cewa, an shirya yin gwanjon NEPA ne saboda:
- Al’ummar Nijeriya na karuwa, don haka akwai bukatar a kara samar da makamashi.
- Raba NEPA zuwa kananan ma’aikatu, domin inganta samar da wutar lantarki, watsawa da kuma rarrabawa.
- Domin zamanantar da fannin wutar lantarki.
- Samarwa tare da gabatar da shigar da kamfanoni masu zaman kansu cikin harka samar da wutar lantarki, wanda zai haifar da ingantaccin biyan bukata na samar da isasshiyar wutar lantarkin.
- Don sanya bangaren wutar lantarkin a kan tafarki kwakkwara mai kuma dorewa tare da cin gashin kanta a fannin.