Sakamakon matsalar ruwan sha da ta addabi Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, yanzu haka yara ne suka mutu sakamakon jigilar ruwan sha a kwale-kwale.
Yara 12 sun kuma nutse a cikin ruwa ba tare da an gano su ba a Gulbin Tulukawa da ke jihar.
- Sauyin Gwamnati: Wainar Da Ake Toyawa A Jihohin Da ‘Yan Adawa Za Su Karbi Mulki
- Yadda Muka Yi Da ‘Yan Bindigar Da Suka Sace Iyalina – Sarkin Kagarko
Daya daga cikin wanda suka tsamo gawarwakin yaran, Sani Aliyu, ya bayyana wa manema labarai cewa, kwale-kwale ya nutse ne bayan yaran sun dauko ruwa daga hayin labuna inda suke samo ruwan wajen masu noman rani da suka gina rijiya da suke amfani da ita.
“Bayan sun loda jarkunan ruwa da su yaran maza da mata a kwale-kwale su na tsakiyar koramar sai kwale-kwalen ya yi ta tangal-tangal, inda take su kai ta fada wa cikin ruwa wasu suka nutse.
“Da hannuna mun samo gawarwaki tara wasu kuma har zuwa yau ba mu samo su ba,” in ji Aliyu.
Aliyu ya kara da cewa, “Wannan ba shi ne karon farko da yara suke mutuwa ba, ko lokacin azumi yara hudu sun mutu saboda debo wa iyayensu ruwa.”
Muhammad Lawal Yusif daya daga cikin wadanda ya rasa diyarsa budurwa ‘yar shekaru 17, wadda aka shirya aurar da ita bayan babbar Sallah, mai suna Zainab da kaninta Aliyu wanda aka tsami gawarwakinsu, ya nuna matukar damuwarsa kan faruwar lamarin.
Muhammad Lawal ya kara da cewa, “Matsalar ruwan sha ne ya sanya muke aiken yaran zuwa hayin gulbi su hau kwale-kwale Naira 10 su sayo jarka Naira 10, sai su kara hawa kwale-kwale Naira 10 a kawo su bakin gaba su fito su kawo gida a yi musu abunci da wanki da shi.”
Mahaifin yaran ya koka sosai ganin yadda a ce Hedikwatar Jihar gwamnati Jihar Zamfara ta gaza samar musu ruwan sha shekara da shekaru kuma akai-akai sai asara rayuka ake yi.
A kan haka ne Lawal ya yi kira ga sabuwar Gwamnatin da za a kaddamar nan da ‘yan kwanaki da ta dubi halin da suke ciki na rashin ruwa domin kawo karshen matsalar.
A binciken da wakilinmu ya yi, ya gano cewa matsalar na ci gaba da faruwa ne sakamakon rashin ba da isashshen kudaden tafiyar da ma’aikatar ruwan a jihar.
Sannan, matsalar wutar lantarki na daya daga cikin dalilin da ya sa ake samun matsalar ruwan.
Kan wannan matsalar, ‘yan jarida sun nemi jin ta bakin Manajan Gudanarwa na ruwa na Gusau, Buhari Dosara, ya bayyana cewa, matsalar wutar lantarki ne babbar matsalar da ke jawo rashin samun wadataccen ruwa a fadin jihar.
Sannan ya koka da da cewa, “Tun daga lokacin gwamnatin Yariman Bakura zuwa yau ma’aikatan ne kadai ke biyan kudin ruwa. Ko su ma babu wanda yake ba da sama da 1000.
“Amma su mutanen gari kyauta suke shan ruwa kuma ga jama’a na karuwa a Gusau ko da yaushe don haka wannan shi ne babban kalubalan da muke fuskanta.”
Manajan ya kara da cewa, “Ka san wata-wata da gwamnati ke ba mu da su ne mu ke maneji wajen sayen gas da kayan sarrafa ruwan don rabawa ga mutanan gari.”
A wani labari kuma, a daidai lokacin da Zamfara ke fama da matsalar ruwa, a makon jiya Hukumar tsaro ta farin kaya ta (NSCDC) ta kama mota dauke da alif wanda za a fitar da shi daga Jihar cikin dare domin kawai Jihar Katsina da Kano.
‘Yan jaridu sun sun tubi, Kwamadan hukumar NSCDC a jihar, Muhammad Mu’azu ya shaida wa manema labarai cewa an kama motar shake da alif na ruwa ne.
“Jami’anmu sun samu nasara kama wannan kaya kuma muna bincike a kai don yanzu haka mun tabbatar da cewa, an kai wasu kayan Katsina da Kano. Mun rubuta wa gwamnatin jiha.”
Ya ce suna kokarin bin sawun inda aka kai alif din domin kwato su.
“Don yanzu haka muna tsare da mai kula da dakin ajiye kayan hukumar ba da ruwan a karkara kuma da sa hannunsa ne aka fidda kayan na Jihar Zamfara domin kai su Katsina da Kano,” in ji kwamanda NSCDC”.
Kwamandan ya nemi manema labarai su ji ta bakin mai kula da dakin ajiyar ma’aikatar hukumar ruwan da ake zargin shi ne ya ba da takardun fidda kayan.
Ya shaida wa manema labarai cewa, shi aikinsa bin umarnin babban manajan ma’aikatar na ba da kaya duk sanda aka nemi ya ba da, kuma yana da shaidar takardar da shi babban manajan ma’aikatar ya sanya hannu na ya b ada kayan zuwa inda za a kai su, kamar yadda jami’an mai kula da ajiye kayan hukumar ruwa na Jihar Zamfara ya shaida da ke fuskantar tuhumar jami’an tsaro.
Kwamadan NSCDC ya tabbatar da cewa duk wanda bincike ya nuna cewa na da hannu a lamarin tabbas za su kama shi kuma za su gurfanar da shi a gaban kotu.