Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya da ke Lokoja, Farfesa Olayemi Akinwumi, ya bayyana cewa dalibai sun hakura da kama hayar dakunan kwanan Dalibai (Hostel) saboda tsoron ta’addancin ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.
Shugaban kwamitin majalisar kasa kan ilimin jami’o’i, Sanata Abubakar Fulata ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Laraba.
- Monguno Ya Maye Gurbin Ndume A Matsayin Mai Tsawatarwar Masu Rinjaye A Majalisa
- Kotu Ta Yi Watsi Da Bukatar Cire Rubutun Ajami A Kudin Nijeriya
Sanarwar ta biyo bayan ziyarar da kwamitin ya kai jami’ar a wani bangare na ayyukan sa ido na majalisar.
Fulata ya bayyana abinda Akinwumi ya ce game da jami’ar, inda ya ce hatta dakunan kwanan dalibai guda biyu da zai dauki mutane kusan 500 babu kowa a cikinsu.
Mataimakin shugaban jami’ar ya ce, hatta hukumar jami’ar na fargabar raba dakunan kwanan daliban saboda tsoron ayyukan masu garkuwa da mutane da ‘yan bindiga.