Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya jaddada buƙatar amfani da manyan na’urorin zamani domin yaƙi da matsalar tsaro a Jihar Zamfara, Arewa da ma Nijeriya baki ɗaya.
Gwamnan Jihar Zamfara da wasu gwamnonin jihohi sun gana da Amina J. Mohammed, Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya a birnin Washington D.C. ranar Juma’a.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris ya fitar ta bayyana cewa taron ya samu halartar gwamnonin jihohin Zamfara, Benuwai, Jigawa, Kaduna, Katsina, Kebbi, da Neja.
Mataimakiyar Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya, Amina J. Mohammed ta yaba wa Gwamnonin kan ƙoƙarin da suke yi na ganin an magance matsalolin yankin.
“Kasancewar ku a nan ya nuna ƙwaƙƙwarar sha’awar da Gwamnonin Arewa ke yi na aiwatar da sauyi a jihohinsu.
Da yake bayyana halin da ake ciki a Zamfara ga Mataimakiyar Babban Sakataren, Gwamna Dauda Lawal ya bayyana muhimmiyar rawar da fasahar zamani za ta iya takawa wajen inganta tsaro da kuma buƙatar haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen amfani da ƙarfin fasahar da ta haɗa da yin amfani da fasahar ƙere-ƙere, na’urorin tantance kwayoyin halitta da kyamarorin sa ido (CCTV).
“Muna nan da matsalolin da dama, amma babban ƙalubalenmu shi ne rashin tsaro, kuma dole ne a yi wani abu a kai.
“Saboda rashin tsaro, noma ya gagara. Muna buƙatar taimako wajen bunƙasa noma ta yadda za mu iya amfani fasaha wajen yaƙi da wannan tada ƙayar baya. Muna fatan samun mafita ga waɗannan matsalolin yayin waɗannan tarukan. Na karɓi mulki a jiha mai cike da rashin aiki tare da ƙarancin ci gaba.
“Na ayyana dokar ta-ɓaci a fannin ilimi da lafiya. Dole ne mu ɗauki matakin gaggawa don magance waɗannan batutuwa masu muhimmanci; in ba haka ba, makomar mu za ta yi muni. Muna buƙatar tallafi mai muhimmanci don shawo kan waɗannan ƙalubalen da kuma tabbatar da kyakkyawar makoma ga jama’armu.”